An yanke wa uwargida hukuncin daurin watanni 6 bayan kona gidan Amaryar tsohon mijinta

An yanke wa uwargida hukuncin daurin watanni 6 bayan kona gidan Amaryar tsohon mijinta

  • Wata Mata mai suna Zainab ibrahim an yanke mata hukuncin daurin watanni shida a wata kotun Shari'ar Musulunci dake Rigasa Kaduna
  • Zainab Ibrahim ta kona gidan Amaryar tsohon Mijinta tare da wasu kayayyakin amfaninta
  • Alkalin kotun Abubakar-Tureta ya bukaci Zainab da ta biya diyyan kayan data kona nai naira Dubu Dari da Talatin da Daya

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zaune a Rigasa, Kaduna a ranar Laraba ta yanke wa wata mata ’yar shekara 34,mai suna Zainab Ibrahim, hukuncin daurin watanni shida saboda kona gidan tsohuwar matar tsohon mijinta, rahoton DN.

Alkalin kotun, Salisu Abubakar-Tureta ya yanke wa Zainab hukuncin ne bayan ta amsa laifukan da suka shafi ke ta haddi da barna ta hanyar wuta.

Alkalin ya bai wa mai laifin zabin tarar N10,000.

Mista Abubakar-Tureta ya kuma umarce ta da ta biya N131,000 a matsayin diyyar kone wasu kayayyakin amfani Mallakar Maryam Ramalan.

KU KARANTA: Alheri kan alheri: Ma’aurata ’yan Najeriya sun samu ’yan biyu shekara 21 suna jiran haihuwa

An yanke uwargida hukuncin daurin watanni 6 bayan kona gidan Amaryar tsohon mijinta
An yanke uwargida hukuncin daurin watanni 6 bayan kona gidan Amaryar tsohon mijinta

KU DUBA: Ana mini barazanar kisa, Shugaban Hukumar EFCC Abdulrashid Bawa

Tun farkon lamarin, lauya mai shigar da kara, Insp Sambo Maigari ya fada wa kotun cewa laifin ya saba wa Sashi na 174 da 373 na Laifi.

Ya ce mai laifin ta amsa cewa ta yi amfani da fetur ne wajen kona gidan sabuwar amaryar saboda Zafin kishi, riwayar Pulse.

Ta nemi ayi mata afuwa

A cikin rokon ta na neman yafiya, ta yi iƙirarin cewa ta kasance mace mai biyayya ga tsohon Mijinta, Har zuwa lokacin da ya sake ta ya auri wata matar.

Ya yi alkawarin dawo da ni gidan aure na amma hakan ya faskara bayan dumbin bauta masa da nayi shi da Iyayensa tsawon shekaru

Ta ce "Gidan Mallakin ta ne ita da yaran ta bakwai."

Asali: Legit.ng

Online view pixel