Hukumar UNICEF ta bukaci a sako daliban Isalmiyya a jihar Neja

Hukumar UNICEF ta bukaci a sako daliban Isalmiyya a jihar Neja

  • Wasu daga cikin dalibai 136 da aka sace daga makarantar Tanko salihu Islamiyya School dake jahar niger suna fuskantar barazanar Rashin Lafiya
  • An sace daliban ne kimanin mako biyu kenan har daya daga cikinsu ma ya rasa ranshi
  • Gwamnatin Jihar ta ce a shirye ta ke wajen ganin ta ceto yaran batare da biyan ko sile ba

Asusun Tallafin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ta yi kira da a gaggauta sakin dalibai 136 da aka sace a wata Makarantar Islamiyya a Jihar Neja Makonni biyu da suka wuce.

UNICEF a wata sanarwa da ta fitar a jiya ta nuna damuwa kan makomar yaran wadanda aka sace su a makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko, Tegina, makonni biyu da suka gabata, rahoton Leadership.

Jami'in da ke kula kuma wakilin UNICEF a Najeriya Rushnan Murtaza, yace:

"Mun yi matukar kaduwa cewa makonni biyu Kenan bayan sace dalibai 136 daga makarantarsu, kuma har yanzu suna rike a hannun wadanda suka sace su,"

KU KARANTA: Alheri kan alheri: Ma’aurata ’yan Najeriya sun samu ’yan biyu shekara 21 suna jiran haihuwa

Hukumar UNICEF ta bukaci a sako daliban Isalmiyya a jihar Neja
Hukumar UNICEF ta bukaci a sako daliban Isalmiyya a jihar Neja
Asali: Twitter

KU DUBA: Ana mini barazanar kisa, Shugaban Hukumar EFCC Abdulrashid Bawa

Murtaza ya ce iyaye sun kasance a cikin jimami game da batan ‘ya’yansu yayin da yayunsu da kannensu ke jimamin rashi yan uwansu Maza da Mata da ke a hannun masu garkuwa da mutane.

Ta yi kira da a sake yaran don su koma ga iyayensu.

Ta bayyana hare-haren da ake kaiwa makarantu da kuma dalibai a matsayin abin tsoro, lura da cewa yara ‘yan kasa da shekaru uku, na ci gaba da zama Makasudin kai hare-hare da makamai da satar mutane.

Unicef ta yi kira ga Gwamnatin Najeriya da ta dauki "dukkan matakai" don kare makarantu a kasar. Har ila yau, ta bukaci gwamnati da ta aiwatar da alkawarin da aka yi a wajen bawa Makarantun Tsaro a Nijeriya a watan Afrilun wannan shekara.

“Dole ne makarantu su kasance wurare masu aminci don yin karatu da ci gaba, Neman Ilimi bai kamata ya zama abu mai haɗari ba, " ya kara.

Wasu cikin yaran sun fara rashin lafiya

An ruwaito cewa wasu daga cikin daliban Islamiyya 136 da aka sace sun kamu da rashin lafiya.

Iyayensu da ke cikin matsanancin damuwa sun ziyarci coci-coci da masallatai don neman a tara kudin fansa.

'Yan ta'addan sun far wa makarantar ne kimanin makonni biyu da suka gabata, inda suka kwashe daliban makarantar 137 a inda sukayi garkuwa dasu.

Sannan sun nemi a biya su N200 miliyan. Sai dai kuma gwamnatin jihar ta ce tana matukar son ganin an sako yaran amma ba tare da ta biya kudin fansa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel