Kwanaki 16 Bayan Sace Daliban Islamiyya, wasu sun kamu da rashin lafiya

Kwanaki 16 Bayan Sace Daliban Islamiyya, wasu sun kamu da rashin lafiya

  • Wasu daga cikin dalibai 136 da aka sace daga makarantar Tanko salihu Islamiyya School dake jahar niger suna fuskantar barazanar Rashin Lafiya
  • An sace daliban ne kimanin mako biyu kenan har daya daga cikinsu ma ya rasa ranshi
  • Gwamnatin Jihar ta ce a shirye ta ke wajen ganin ta ceto yaran batare da biyan ko sile ba

An ruwaito cewa wasu daga cikin daliban Islamiyya 136 da aka sace a makarantar Tanko Salihu dake karamar hukumar Rafi a jihar Neja sun kamu da rashin lafiya.

Iyayensu da ke cikin matsanancin damuwa sun ziyarci coci-coci da masallatai don neman a tara kudin fansa.

'Yan ta'addan sun far wa makarantar ne kimanin makonni biyu da suka gabata, inda suka kwashe daliban makarantar 137 a inda sukayi garkuwa dasu. Sannan sun nemi a biya su N200 miliyan. Sai dai kuma gwamnatin jihar ta ce tana matukar son ganin an sako yaran amma ba tare da ta biya kudin fansa ba.

Daga baya, an bayar da Rahoton cewa daya daga cikin yaran da aka sace, dan shekara uku, ya mutu bayan 'yan fashin sun yi watsi da shi saboda rashin bin yadda suke so.

An fahimci cewa yan fashin sun tuntubi shugaban makarantar, Alhassan Garba Abubakar, inda suka bayyana rashin lafiyar yaran.

'Yan fashin sun fada wa shugaban makarantar cewa duk daliban da aka sace suna nan da ransu amma wasu daga cikinsu sun kamu da rashin lafiya saboda yanayin da suka tsinci kansu a cikin makonni biyu da suka gabata.

Gwamnan Neja
Kwanaki 16 Bayan Sace Daliban Islamiyya, wasu sun kamu da rashin lafiya Hoto: Press Secreatry Joel
Asali: Facebook

Shugaban makarantar ya kuma shaida wa Gidan Jaridan LEADERSHIP cewa ‘yan fashin sun sassauto da Kudin fansar daga Naira miliyan 200 zuwa miliyan 150.

"Ban dade da gama Magana da su ba ('yan fashin) kuma sun tabbatar da cewa duka daliban suna raye amma ba za mu yi tsammanin ba za su yi rashin lafiya ba a halin da suke ciki tare da' yan fashin," yace.

Ya ce iyayen yaran da aka sace sun ci gaba da tara kudi don biyan bukatun ‘yan fashin.

"Suna bin coci-coci da masallatai don neman kudin fansa," in ji shi.

“Adadin da aka tara ya zuwa yanzu ko kusa bai kama kafa da abin da‘ yan fashin ke nema ba kafin su saki Yaran.

“Bana Daya daga cikin kwamitin iyayen da ke zuwa coci-coci da masallatai don neman gudummawan kudin fansan da za a biya; don haka ba zan iya fada muku ainihin adadin kudin da aka tara zuwa yanzu ba, ”inji shi.

Da aka tambaye shi ko sun samu hadin kai da Gwamnatin Jihar don ganin an hanzarta sakin daliban, sai ya ce, “Gwamnatin ta tura shugaban karamar hukumar Rafi kuma sun yi ikirarin cewa suna yin wani abu; ba mu san abin da suke yi ba."

Sakataren gwamnatin jihar Neja, Alhaji Ahmed Matane, ya ce 'yan fashin na iya amfani da kowace irin dabara don ganin sun tayar da hankulan iyayen yaran don biyan kudin fansa.

Hukumar ta SSG ta ce, gwamnati na ci gaba da tattaunawa da iyalan daliban da aka sace, kuma ta ba su kwarin gwiwa cewa ana ci gaba da kokarin ganin an kubutar da daliban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel