NDLEA ta kame kwalban kodin 100,000 a tashar ruwan Onne

NDLEA ta kame kwalban kodin 100,000 a tashar ruwan Onne

  • Hukumar ta kuma bankado hodar Ibilis mai nauyin kilo 146.95 a filin jiragen sama
  • Babu wanda ya gabatar da kansa a matsayin wanda ya mallaki kwalaben da aka kwato
  • Da a ce kwalaben sun tsallaka da za su haukata matasa da dama

Hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta kasa, (NDLEA) ta kwato kwalaben kodin har guda dubu 100,000, masu nauyin kilo 15,325 a tashar jiragen ruwa na Onne da ke Fatakwal a Jihar Ribas.

An jibge kwalaben ne cikin katan-katan har 500 sannan aka boye su a wata kontaina mai lamba MRKU 1565305, kirar kasar India.

A ranar Alhamis ce aka bankado kontainar cikin wani dakin ajiyar kaya yayin wani samamen hadin gwiwa tsakanin jami’an hukumar da takwarorinsu na kwastam.

Daraktan yada labarai na hukumar Femi Babafemi, shi ya bayyana hakan a Abuja ranar Asabar a jawabin da Legit ta samu.

Ya fada cewa:

“Bankado kwalaben ya biyo bayan tsegunta wa hukumar da bayanan sirri, wanda ya haifar da aka dakatar da kontainar sannan aka kai ta dakin ajiyar kwastam a tashar jiragen ruwan.
“Har yanzu babu wani mutum ko dillalin da ya fito ya nuna cewa kayan nasa ne, sai dai muna kokarin bankado wanda ya mallaki kayan domin bincike tare da gurfanar da shi gaban shari’a.”

KU DUBA: A shirya kuri’ar raba gardama, a taimaka wa Ibo su balle daga Najeriya: Kungiyoyin Arewa

NDLEA ta kame kwalban kodin 100,000 a tashar ruwan Onne
NDLEA ta kame kwalban kodin 100,000 a tashar ruwan Onne

KU KARANTA: Buhari ya ciwo bashin fiye da biliyan 10 a kowace rana cikin shekara shida na mulkinsa

A wani lamarin mai nasaba da wannan, jami’an hukumar NDLEA da ke aiki a tashar jiragen saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, sun kwato wata hodar Ibilis mai nauyin kilo 146.95, a bangaren dakon kaya na tashar.

Hukumar ta ce kunshin hodar wanda aka yi badda sawun cewa ganyen shayin ‘Green Tea’ ne jirgin Ethiopian Airline ne ya shigo da shi daga Addis Ababa babban birnin kasar Habasha.

Shugaban hukumar ta NDLEA, Birgediya Janal Mohamed Buba Marwa (Mai ritaya) ya jinjina wa hadin kan da hukumar ke samu daga takwarorinta na tsaro, inda ya yi kiran da su kara zage damtse domin ganin an raba Najeriya da miyagun kwayoyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel