Masu ruwa da tsaki sun bukaci Gwamnati ta shiga tsakani a batun dakatar da safarar albasa Kudu

Masu ruwa da tsaki sun bukaci Gwamnati ta shiga tsakani a batun dakatar da safarar albasa Kudu

- An yi zargin ’yan bindiga sun kwace wasu tireloli biyu dauke da albasa na mambobin kungiyar a kan hanyarsu ta zuwa Kudu maso Gabas.

- Shugaban kungiyar masu sarrafa shinkafa na kasa, (RIMAN), Mista Peter Dama, ya ce lamarin abin damuwa ne matuka

-A cewarsa, matakin zai shafi manoman da kuma masu amfani da albasar kasancewar ta mai saurin lalacewa

Masu ruwa da tsaki a bangaren noma sun bukaci Gwamnatin Tarayya da ta tsoma baki a shirin da kungiyar manoma da dillalan albasa ta kasa ke yi na dakatar da safarar albasa zuwa yankin Kudancin kasar nan.

Shugaban kungiyar na kasa, Mista Aliyu Umar, a ranar 30 ga watan Mayu ya bayyana cewa dakatarwar da mambobin kungiyar za su yi nada manufar takaita hare-haren da ake kaddamarwa kan tirelolin albasa na ’ya’yan kungiyar da suke kai wa zuwa Kuadancin Najeriya.

An yi zargin ’yan bindiga sun kwace wasu tireloli biyu dauke da albasa na mambobin kungiyar a kan hanyarsu ta zuwa Kudu maso Gabas.

Wadansu daga cikin masu ruwa da tsakin da suka yi magana da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ranar Laraba sun ce matakin dakatar da safarar albasar ba shi bane maslaha ga dukkanin bangarorin biyu – manoman da kuma masu saya, rahoton Vanguard.

KU KARANTA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Masu ruwa da tsaki sun bukaci Gwamnati ta shiga tsakani a batun dakatar da safarar albasa Kudu
Masu ruwa da tsaki sun bukaci Gwamnati ta shiga tsakani a batun dakatar da safarar albasa Kudu

KU DUBA: Gwamnatin Amurka ta bukaci a gaggauta dawo da Tuwita Najeriya

Shugaban kungiyar masu sarrafa shinkafa na kasa, (RIMAN), Mista Peter Dama, ya ce lamarin abin damuwa ne matuka.

Ya yi kira ga Ma’aikatar Masana’antu da Kasuwanci tare da Ma’aikatar Ayyukan Gona da Raya Karkara da su shiga tsakani domin warware kiki-kakar.

A cewarsa, matakin zai shafi manoman da kuma masu amfani da albasar kasancewar ta mai saurin lalacewa.

Wacce ta kafa kungiyar ci gaban manoman mata ta kasa (WOFAN), Misis Salamatu Garba, ita ma ta yi kiran gwamnatin da ta gaggauta shiga tsakani domin kauce wa gurgunta tattalin arziki da matakin dai zai haifar.

Sannan ta yi Allah wadai da kwace tirelolin albasar da aka yi a Kudancin Najeriyar inda ta yi kira ga ’yan Najeriya da kada su bari wadansu tsirarun miyagun mutane su haddasa husuma ga sauran jama’a.

“Ainihin manoman na can a kauyuka amma ’yan kasuwar da ke jin dadin abin da ke faruwan watakila sune ke iza wutar daga yankin Arewaci da Kudancin Najeriya,” inji Misis Ramatu Garba.

Legit ta zanta da wani dan kasuwan albasa a garin Abuja, Auwal Bello, ya bayyana amincewarsa da hukuncin da uwar kungiyar manoma da yan kasuwan albasa ta yanke.

Ya bayyana cewa basu ki Albasar tayi kwantai ba.

"Tun da mutanen nan sun yi sau daya, sau biyu, gwamnati bata dau mataki ba. Muna goyon bayan mutanen nan su biyamu kayan da suka kona mana, idan suka biyamu sai mu cigaba da kasuwanci da su, " yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel