Yanzu-Yanzu: Kungiyar Ma'aikatan Shari'a, JUSUN, Ta Janye Yajin Aiki

Yanzu-Yanzu: Kungiyar Ma'aikatan Shari'a, JUSUN, Ta Janye Yajin Aiki

- Bayan watanni ana ta tattaunawa tsakanin FG da kungiyar JUSUN, yajin aikin aikin da aka fara a watan Afrilu ya zo karshe

- Kungiyar ta sanar da janye yajin aikin ne a ranar Laraba 9 ga watan Yunin shekarar 2021

- JUSUN ta dauki wannan matakin ne bayan taro mai tsawo da ta yi da kwamitin koli na shari'a, NJC da Alkalin Alkalai na kasa CJN

Ƙungiyar ma'aikatan Shari'a ta Najeriya, JUSUN, a ranar Laraba, ta dakatar da yakin aikin da ta kwashe kimanin watanni biyu tana yi.

Kungiyar ta ce ma'aikatan ta za su koma aiki a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Yanzu-Yanzu: Kungiyar Ma'aikatan Shari'a, JUSUN, Ta Janye Yakin Aiki
Yanzu-Yanzu: Kungiyar Ma'aikatan Shari'a, JUSUN, Ta Janye Yakin Aiki. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Matar El-Rufai: A Shirye Nake In Mutu Hannun Masu Garkuwa, Kada a Biya Kuɗin Fansa Idan An Sace Ni

The Punch ta ruwaito cewa a watan Afrilu ne JUSUN ta fara yajin aikin na sai Baba ta gani a duk fadin kasar kan hana su 'yancin kansu musamman abin da ya shafi ɓangaren kudi kamar yadda doka ya basu 'yancin kuma kotu ta tabbatar a Janairun 2014.

JUSUN ta yi watsi da rokon da Alkalin Alƙalai na ƙasa ya yi mata na cewa ta janye yajin aikin.

Kungiyar ta dauki matakin janye yajin aikin ne ne bayan taro mai tsawo da ta yi da kwamitin koli na shari'a, NJC da Alkalin Alkalai na kasa CJN

A wani rahoton daban kun ji cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta dauki sabbin ma'aikata 10,000 a ma'aikatu da hukumomin jihar a yayin da ta ke rage yawan ma'aikata a wasu hukumomin, rahoton The Cable.

Muyiwa Adekeye, mashawarcin gwamna Nasir El-Rufai kan watsa labarai ne ya bada wannan sanarwar a ranar Litinin.

Adekeye ya ce za a dauki ma'aikatan ne cikin wadanda aka tantance yayin aikin daukan sabbin ma'aikata a jihar kamar yadda Sun News ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel