Buhari Mutumin Allah ne, Mutum ne Mai Daraja, Inji Primate Ayodele

Buhari Mutumin Allah ne, Mutum ne Mai Daraja, Inji Primate Ayodele

- Shugaba Buhari ya samu yabo daga Primate Ayodele wanda yayi ikirarin cewa shugaban ba zai yi yunkurin ci gaba da rike mulki ba a karo na uku

-Ayodele ya kuma yi ikirarin cewa tun farko ya gargadi ‘yan Nijeriya cewa wa’adin Buhari na biyu zai yi tsauri

-Bayan nan malamin ya Alakanta 'yan siyasa akan sace-sacen mutane da kashe-kashen da ke faruwa a kasar

Shehi kuma babban malamin cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Lagos, Primate Elijah Ayodele, ya yi ikirarin cewa ya kamata yan Najeriya su watsar da tunanin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai so ya zarce kan mulki karo na uku.

A cewarsa, shugaban kasar bawan Allah ne kuma babban mutum ne wanda zai yi biyayya ga kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ayodele ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da Kafar yada labarai na Legit.ng a ofishin sa da ke jihar Legas.

Ya ce a baya ya fada wa ‘yan Najeriya cewa abubuwa ba za su yi dadi ba a wa’adin mulkin Buhari karo na biyu kuma hasashen nasa ya tabbata.

Malamin ya cigaba da cewa dole ne jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta lura da cewa akwai abubuwa da yawa da ba daidai ba a Fadar Shugaban Kasa.

KU KARANTA: Masu neman raba kasar nan shaidanu ne, Mai Alfarma Sarkin Musulmi

Buhari Mutumin Allah ne, Mutum ne Mai Daraja, Inji Primate Ayodele
Buhari Mutumin Allah ne, Mutum ne Mai Daraja, Inji Primate Ayodele
Asali: Original

KU DUBA: Gwamnatin Najeriya na shawarar yanke hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da lalata layin dogo

Primate Ayodele ya kuma yi iƙirarin cewa akwai wasu ɓoyayyun al'amura da ya kamata gwamnati ta bayyana wa duniya cewa ba su yi ba.

Sace sacen mutane da rashin tsaro

Shehin malamin ya ce dalilan duk wadannan sace-sacen mutane da rashin tsaro a kasar shine villa ba ta fahimci abun bane.

Ayodele ya kuma zargi ‘yan siyasa akan sace-sacen mutane da kashe-kashen da ke faruwa a kasar.

"Shugaba Buhari mutum ne mai girma,Shugaba Buhari bawan Allah ne, zai girmama kalamansa, ba zai kara wa'adi na uku ba. Ba ma zai fara tunanin haka ba, Ya ma riga ya gaji tuni," Ayodele yace.

"Ba zai iya yin kaura daga kasar ba.Ya ce: "Ba zan iya kaura daga Najeriya ba.A nan zan mutu. Zan tsaya a nan, in mai da ita abun alfaharina in mutu a Najeriya kuma a binne ni a Najeriya."

A wata sanarwa mai cike da hikima a ranar Lahadi, 21 ga Maris, Primate Ayodele ya ce Nijeriya na gab da fuskantar gagarumar zanga-zanga da karancin abinci.

Shahararren malamin addinin kiristanci ya ci gaba da cewa yana hango mummunan yanayi na tattalin arziki da zai zo tare da rashin tsaro a duk fadin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel