Kisan Gulak: Fargaba a APC yayin da jam’iyyar reshen Adamawa ta aika gagarumin sako ga Gwamna Uzodimma

Kisan Gulak: Fargaba a APC yayin da jam’iyyar reshen Adamawa ta aika gagarumin sako ga Gwamna Uzodimma

- Jam’iyyar APC a jihar Adamawa ta zargi gwamna Uzodimma da yunkurin rufe batun kisan Gulak

- Ibrahim Bilal, shugaban APC jam’iyyar APC reshen jihar, ya yi kira ga gwamnan Imo da ya zakulo wadanda suka yi kisan

- An kuma bukaci Shugaba Buhari da ya sanya baki tare da tabbatar da cewa wadanda ke da alhakin kisan jigon na APC ba su tsere wa hukunci ba

Babin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Adamawa ta bukaci gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma da ya fito da wadanda suka kashe Ahmed Gulak.

Ibrahim Bilal wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC na Adamawa ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Alhamis, 3 ga watan Yuni, a Yola, babban birnin jihar, jaridar The Guardian ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: 2023: Babu sunan Tinubu yayinda kungiyar arewa tace tana duba yiwuwar marawa Amaechi, Umahi da sauransu baya

Kisan Gulak: Fargaba a APC yayin da jam’iyyar reshen Adamawa ta aika gagarumin sako ga Gwamna Uzodimma
Kisan Gulak: Fargaba a APC yayin da jam’iyyar reshen Adamawa ta aika gagarumin sako ga Gwamna Uzodimma Hoto: @Hope_Uzodimma1
Asali: Twitter

An kashe Gulak, sanannen jigo a jam’iyyar APC a Owerri, babban birnin jihar Imo, a ranar Lahadi, 30 ga watan Mayu.

A cikin sanarwar wacce ke nuni da mummunan lamarin na iya haifar da baraka a cikin APC, Bilal ya zargi gwamnan da kokarin share lamarin a karkashin kasa.

KU KARANTA KUMA: Gumi ga FG: Ku sasanta da yan bindigar da suka tuba, ku yi amfani da su wajen yakar wadanda suka ki saduda

Ya yi zargin cewa wadanda suka yi niyyar kashe 'yan arewa a yankin kudu maso gabashin kasar ne suka shirya kisan Gulak.

Bilal ya bayyana shigar da dalilai na siyasa da gwamna Uzodimma yayi a cikin mutuwar Gulak a matsayin abin shakku.

Ya ce:

"Tunda ya danganta dalilan siyasa da shi, a matsayinsa na babban jami'in tsaro na jihar, ya kamata ya gabatar da wadanda suka aikata hakan."

Ya kamata Buhari ya sa baki

Shugaban APC na Adamawa ya kuma yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya yi amfani da kyawawan ofisoshinsa don tabbatar da adalci ga Gulak, kamar yadda Sahara Reporters ta bayyana.

Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta bi sahun Indigenous People of Biafra (IPOB) tare da murkushe kungiyar ta hanyar yin amfani da dukkan karfin ta.

Sabanin ikirarin na gwamna Uzodimma, Bilal ya zargi haramtacciyar kungiyar da kashe Gulak.

A wani labarin, hukumar 'yan sanda ta tabbatar da nadin Alkali Baba a matsayin babban Sufeto Janar na 'yan sanda (IGP), jaridar Leadership ta ruwaito.

Legit.ng ta tuna cewa a ranar 6 ga Afrilu ne Buhari ya nada Usman Baba a matsayin mukaddashin Sufeto Janar na 'yan sanda.

Jaridar The Punch ta kuma ruwaito cewa an yanke hukuncin ne a taron hukumar wanda shugaba Buhari ya jagoranta a ranar Juma’a, 4 ga watan Yuni, a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel