Da Ɗumi-Ɗumi: MTN, Airtel, Glo Sun Rufe Damar Shiga Twittter a Najeriya

Da Ɗumi-Ɗumi: MTN, Airtel, Glo Sun Rufe Damar Shiga Twittter a Najeriya

- Kamfanonin sadarwa a Najeriya sun rufe damar hawa dandalin sada zumunta na twitter a faɗin ƙasar

- Kamfanonin da suka haɗa da MTN, Glo, Airtel, 9mobile da sauransu, sun yi haka ne bisa umarnin NCC

- Gwamnatin tarayya ta dakatar da amfani da Twitter a Najeriya biyo bayan wata taƙaddama tsakanin su, inda twitter ta goge rubutun shugaba Buhari

Kamfanonin sadarwa a Najeriya kamar MTN, Glo, Airtel da 9mobile sun fara rufe amfani da damar shiga dandalin sada zumunta twitter, kamar yadda Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: NLC Ta Aike Wa Buhari Wasiƙa, Tayi Barazanar Sake Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa a Kan El-Rufa’i

Kamfanonin sun ce sun samu saƙon umarni daga hukumar sadarwa ta ƙasa NCC cewa su tsayar da damar shiga twitter a ƙasa biyo bayan umarnin gwamnatin tarayya na dakatar da shafin.

Yan Najeriya masu amfani da twitter sun wayi garin ranar Asabar ba tare da samun damar amfani da shafinsu na twitter ba, yayin da wasu ke amfani da wata manhajar sadarwa domin shiga shafin su.

Da Ɗumi-Ɗumi: MTN, Airtel, Glo Sun Rufe Damar Shiga Twittter a Najeriya
Da Ɗumi-Ɗumi: MTN, Airtel, Glo Sun Rufe Damar Shiga Twittter a Najeriya Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kamfanonin sadarwar Najeriya baki ɗaya sun bayyana ƙarƙashin ƙungiyar su cewa sun fara dakatar da damar amfani da twitter a wani jawabi da suka fitar ranar Asabar.

Jawabin wanda a ka yiwa take da "Umarnin dakatar da mafani da twitter a Najeriya" wanda shugaban ALTON, Gbenga Adebayo, da sakatarensa, Gbolahan Awonuga, suka sanya wa hannu.

KARANTA ANAN: Gwamna Ya Dakatar da Biyan Mafi Ƙarancin Albashi, Ya Zabtare Albashin Ma’aikatan Jiharsa

Wani sashin jawabin yace: "Mu, Ƙungiyar kamfanonin sadarwa ALTON, mun tabbatar da mambobin mu sun samu umarni daga NCC cewa su dakatar da bayar da damar amfani da twitter."

"Mambobin mu sun yi biyayya ga umarnin da hukumar sadarwa NCC ta basu, kuma zasu cigaba da biyayya ga dukkan umarnin da hukumomi da masu faɗa aji suka basu a Najeriya."

A wani labarin kuma Najeriya Zata Samar Da Manyan Wayoyin Hannu Ga Ƙasashen Africa, Pantami

Ministan Sadarwa, Dr. Isa Pantami, yace Najeriya zata iya samar da manyan wayoyin hannu da layukan waya ga ƙasashen Africa.

Ministan yace nan da shekara 2 zuwa 3, kashi 60-70% na abubuwan da muƙe buƙata a ɓangaren sadarwa za'a samar dasu a cikin ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel