Hukuncin Wanda Ya Sadu Da Matarsa Tana Cikin Jinin Haila, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Hukuncin Wanda Ya Sadu Da Matarsa Tana Cikin Jinin Haila, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa babban Malamin addinin Musulunci ne mazaunin jihar Kano wanda ya fi shahara wajen bayani kan mas'alolin rayuwa da zamantakewa.

A wannan karo, Malamin ya yi bayanin cikin sauki abubuwan da ya kamata mutum ya sani game da mutumin da ya sadu da iyalinsa yayinda jinin al'ada.

Hukuncin wanda ya sadu da matarsa tana cikin jinin haila, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Babu saɓani tsakanin malamai cewa haramun ne mutum ya sadu da matarsa tana al’ada.

Idan kuwa mutum ya sadu da matarsa tana haila, to ɗayan abu huɗu ne ya faru.

Ko dai jahili ne bai sani ba ya sadu da ita da jahilci, ko kuma kuskure ya yi, ya ɗauka jinin bai zo ba sai da ya sadu da ita ya ga jini, ko kuma ganganci ya yi, ya san tana jinin ya je ya sadu da ita, ko kuma dole aka yi masa ya sadu da matarsa alhali tana cikin al’ada ɗin, ko kuma ita matar ce ta ɓoye masa cewa tana jinin haila, bai sani ba sai da ya sadu da ita, sannan ya gano.

Kara karanta wannan

Dalilin Na Yasa Muka Nemi Afuwar Yan Najeriya Kan Yadda Muka Gudanar Da Mulki, Aisha Buhari

To in dai ya sadu da ita da gangan, wannan shi ne ya aikata savo, domin ya keta dokar da Allah ﷻ Ya shimfiɗa masa cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

وَلاَتَقْرَبُوهُنَّ حَتَّى يَطْهُرْنَ

Ma’ana, “Kar ku kusanci mata har sai sun yi tsarki.”

ME YA KAMATA WANDA YA AIKATA HAKAN YA YI?

Ya yi nadama, ya tuba, ya yi alƙawarin ba zai sake komawa ba. Wato, sai an sami abu uku: nadama, ya daina, ya yi alƙawarin ba zai sake ba.

Shin akwai kaffara a kansa?

Akwai hadisin da ya zo cewa, “Wanda ya sadu da matarsa tana cikin jinin al’ada, sai ya yi sadaka da dinare ko rabin dinare, shi ne kaffararsa.”

Kuma ya tabbata daga ruwayar Abdullahi ɗan Abbas (رضي الله عنه) cewa ya yi fatawa da haka kuma ba wai Annabi ﷺ ne ya faɗa ba, shi ya yi fatawa da hakan.

Kara karanta wannan

Yadda Matar Aure Ta Zama Mai Aikin Goge-goge Don Tura Mijinta Makaranta A Kasar Waje, Bidiyon Ya Yadu

Don haka abin da ake biya gwargwadon wannan kaffara dinare ko rabin dinare, dinare shi yake dai-dai da gram huxu da ɗigo biyar, wanda kuɗinsa yake dai-dai da naira dubu sittin, (6o,ooo) da aka ƙiyasta a yanzu.

Saboda dubu sittin sau dubu ɗaya, shi ne miliyan sittin, wanda shi yake ba da diyyar rai a wannan lokaci. Sai mutum ya ba da wannan bayan ya tuba ya yi kaffara.

Hukuncin wanda ya sadu da matarsa tana cikin jinin haila, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Hukuncin wanda ya sadu da matarsa tana cikin jinin haila, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Hoto: Mal.Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

SHIN AKWAI BAMBANCI TSAKANIN JININ CUTA DA JININ HAILA?

Malamai sun faɗi wasu bambance-bambance da yawa da za a iya gane wannan jinin haila ko cuta ne, amma ga abubuwa guda shida da aka fi ambata:

1. Dangane da siffar jinin, shi jinin haila ya fi karkata zuwa ga siffar baƙi, shi kuma jinin cuta ya fi karkata zuwa ga ja, ko kuma ɗan fatsi-fatsi na yalo-yalo.

2. Shi jinin haila yana da kauri, shi kuma jinin ciwo ba shi da kauri.

Kara karanta wannan

Wani Mutumi Ya Mutu a Ɗakin Hotel Bayan Ya Shiga da Wata Mace Zasu Ji Dadi

3. Shi jinin haila yana da wari, shi kuma jinin istihadha (jinin cuta) ba shi da wari.

4.Jinin haila yana fita ne daga cikin mahaifa, shi kuma jinin cuta yana fita ne daga gefen mahaifa. Wata jijiya ce ana kiran ta “Iziq” ita take fitar da shi.

5.Jinin haila jini ne na ɗabi’a wanda yake fita a lokuta sanannu, shi kuma jinin ciwo jini ne na rashin lafiya wanda ba shi da wani lokaci sananne, kowanne lokaci yana iya fita. Dangane da yawansa ko kwanakinsa, zai iya fita a kowanne lokaci.

6. Jinin haila ba ya daskarewa idan ya fito waje, domin ya riga ya gama daskarewa a cikin mahaifa. Idan ya fito waje sai ya wargaje, shi kuwa jinin cuta bayan ya fito waje sai ya daskare.

Waɗannan su ne alamomi guda shida waɗanda ake bambance tsakanin jinin haila da jinin cuta, amma abin yana iya bambanta daga wani lokaci zuwa wani lokaci ko wuri zuwa wani wuri ko mace zuwa wata macen ko yanayi zuwa wani yanayin, domin wannan ba nassi ba ne ballantana a ce ba ya sauyawa.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Mutane Sama da 10 Sun Mutu Yayin da Wani Ibtila'i Ya Auka Musu a Jihar Arewa

Idan abu ya yi tsanani aje asabiti, domin tantancewa.

Allah ne masani

Asali: Legit.ng

Online view pixel