Dakatar Da Twitter: Shehu Sani Ya Bayyana Hanya Mafi Sauki Don Hawa Twitter

Dakatar Da Twitter: Shehu Sani Ya Bayyana Hanya Mafi Sauki Don Hawa Twitter

- Shehu Sani ya shawarci 'yan Najeriya kan cewa akwai hanyoyin da za su iya bi su yi Twitter

- Ya ba mutanen kudu maso kudu da na Legas har ma da 'yan Arewa shawarin yadda za su yi

- Shawarin nasa na zuwa ne biyo bayan umarnin dakatar da Twitter da gwamnatin Najeriya ta yi`

Tsohon sanata daga yankin Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya bayyana wata hanya mafi sauki ga mutanen da ke son hawa shafin Twitter duk da hanin da aka yi.

Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnatin Najeriya ta dakatar da ayyukan kafar sada zumunta ta Twitter bisa goge wani rubutu da shugaban kasar ya yi, lamarin da ya jawo cece-kuce.

Shawarar da Shehu Sani ya bayar, ta tsaya ne kan 'yan Najeriya dake rayuwa a jihar Legas, da kuma duk wadanda ke rayuWa a jihohin dake kusa da iyakokin kasa.

KU KARANTA: Ya kamata Twitter ta bar Najeriya: Adamu Garba ya caccaki Twitter saboda Buhari

Dakatar Da Twitter: Shehu Sani Ya Bayyana Hanya Mafi Sauki Don Hawa Twitter
Dakatar Da Twitter: Shehu Sani Ya Bayyana Hanya Mafi Sauki Don Hawa Twitter Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A wani rubutu da ya yi a shafinsa, kuma Legit.ng Hausa ta gano, Shehu Sani ya bayyana shawarin nasa in da yake cewa:

"Idan kana zaune a Legas kuma kana son yin rubutu a Twitter, kawai ka je Cotonou, yi rubutunka ka dawo."

A wani rubutun kuwa:

"Ku dake daga Kudu maso Kudu wadanda suke son yin Twitter, ku dauki kwalekwale ta hanyar Koginku zuwa Kamaru, kuyi Twitter ku dawo."

Ya sake cewa:

"Ku dake daga Arewa, idan kuna son yin Twitter, sai ku hau jirgin kasa zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar, ku yi Twitter ku koma gida."

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Hukumar Jarrabawar NECO Ta Nada Sabon Shugaban Riko

A wani labarin daban, Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, kamfanonin sadarwa a Najeriya sun ce sun samu umarni daga Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) don aiwatar da dakatar da ayyukan karamin shafin yanar gizo na Twitter.

Kamfanonin da ke aiki a karkashin kungiyar masu lasisi na kamfanonin sadarwar na Najeriya (ALTON), sun ce sun gudanar da aikin tantance bukatar bisa ga kyakkyawan tsarin duniya.

Shugabanta, Gbenga Adebayo, a cikin wata sanarwa, ya ce:

“Mu, kungiyar masu lasisi na kamfanonin sadarwar na Najeriya (ALTON), muna son tabbatarwa cewa mambobinmu sun karbi umarni daga Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), mai kula da masana'antun da su dakatar samun damar isa ga Twitter."

Asali: Legit.ng

Online view pixel