Hotunan Muggan Makaman Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Daga Hannun Masu Garkuwa Da Ƴan Bindiga

Hotunan Muggan Makaman Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Daga Hannun Masu Garkuwa Da Ƴan Bindiga

- Rundunar yan sanda ta yi holen wasu mutane 81 da aka kama kan zargin laifuka daban-daban

- An kama wadanda ake zargin ne da laifuka irinsu fashi, garkuwa da sauransu daga watan Afrilu zuwa Mayun 2021

- A baya-bayan nan an samu karin muggan laifuka a kasar da kuma kai wa gine-ginen gwamnati hari musamman a kudancin Nigeria

Rundunar yan sandan Nigeria, a ranar Laraba, ta yi holen wasu da ake zargin masu garkuwa, yan bindige ne da aka kama daga watan Afrilu zuwa Mayun 2021, Channels TV ta ruwaito.

Sanarwar da mai magana da yawun yan sanda, Frank Mba ya fitar da cewa ana zargin wadanda aka kama da laifuka daban-daban da suka hada da garkuwa da mutane fashi da makami, mallakar makami ba tare da izini ba, kera lambobi ba bisa ka'ida ba da sauransu.

Hotunan Muggan Makaman Da AKa Ƙwato Daga Masu Garkuwa Da Ƴan Bindiga
Hotunan Muggan Makaman Da AKa Ƙwato Daga Masu Garkuwa Da Ƴan Bindiga. Hoto: @ChannelsTV
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An Kashe Sufetan Ƴan Sanda Da Wasu Mutane Shida a Ƙauyen Katsina

A cewar kakakin yan sandan, wasu daga cikin abubuwan da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da bindigu daban-daban guda 45 kamar AK-47 guda 17, Ak-47 na gida Nigeria guda 20, GPLG guda daya da sauransu.

Mr Mba ya bada tabbacin cewa kallubalen tsaro da ake fama da shi a kasar zai sa a gano bajintar rundunar ta yan sanda.

A baya-bayan nan, an samu karuwar laifuka irin su garkuwa da mutane da hare-haren yan bindiga a sassa daban-daban na Nigeria.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Shafin Twitter Ya Goge Gargaɗin Da Buhari Ya Yi Wa 'Ƴan IPOB'

Satar dalibai da yawa a kasar shima ya fara zama ruwan dare inda a baya-bayan nan yan bindiga sun sace dalibai da ba a tantance adadinsu ba daga makarantar islamiyya a Tegina, jihar Niger.

Bayan hakan ana ta kai hare-hare ofisoshin hukumar zabe na kasa INEC, ofishin yan sanda, gidajen gyaran hali da sauransu.

A wani labari daban, wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe mataimakin sufetan yan sanda, AIG, Christopher Dega (mai murabus) a birnin Jos, jihar Plateau kamar yadda TVC News ta ruwaito.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Plateau, Ubah Ogaba, ya tabbatar da afkuwar hakan a ranar Laraba 2 ga watan Yunin 2021.

Rahotanni sun ce an yi ta harbinsa da bindiga a kirjinsa ne har sai da jini ya yi ta zuba daga jikinsa ya kuma ce ga garin ku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel