Daga lokacin AbdulSalam zuwa Yanzu: Adadin kudin satar Abacha da aka samu nasarar kwatowa

Daga lokacin AbdulSalam zuwa Yanzu: Adadin kudin satar Abacha da aka samu nasarar kwatowa

Marigayi Janar Sani Abacha ya yi mulkin Najeriya daga 1993 zuwa 1998 da ya mutu.

Yana daga cikin jerin shugabannin Najeriya da suka mutu kan ragamar mulki.

Tun bayar wafatinsa, Najeriya na cigaba da gano wasu kudade da ya boye a kasashen waje wanda aka fi sani da kudin satar Abacha.

Wannan rahoto na lissafa adadin kudaden satar Abacha da aka samu nasarar kwatowa daga wadannan kasashe:

1. Abdulsalami Abubakar ($750 million)

Abdulsalami Abubakar ya dane karagar mulki bayan mutuwar Abacha a 1998 kuma ya shirya komawar Najeriya mulkin Demokradiyya.

Ya kwato kudi $750 million daga wajen iyalan Abacha.

2. Olusegun Obasanjo

Tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya mulki Najeriya tsakanin 1999 da 2007.

A shekarar 2000, ya kwato kudi $64 million da Abacha ya boye a kasar Swizalan.

Obasanjo ya kwato $1.2 billion ta wani harka na iyalan Abacha a 2002.

A 2003, Obasanjo ya sake kwato kudade $160 million daga Jersey da Birtaniya, sannan $88 million daga Swizalan.

A 2005, Obasanjo ya sake kwato $461 million daga Swizalan, hakazalika a 2006 $44 million.

KU KARANTA: Kyakkyawar budurwa yar Arewa wacce ta fara tukin jirgi tun tana shekara 17

Daga lokacin AbdulSalam zua Yanzu: Adadin kudin satar Abacha da aka samu nasarar kwatowa
Daga lokacin AbdulSalam zua Yanzu: Adadin kudin satar Abacha da aka samu nasarar kwatowa
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

3. Goodluck Jonathan

A 2014, tsohon shugaban Jonathan ya smau nasarar kwato $227 million daga kasar Liechtenstein

4. Muhammadu Buhari

A 2018, Shugaba Muhammadu Buhari ya kwato $322 million daga Swizalan, sannan a 2020, ya samu nasarar kwato $308 million daga Jersey/USA.

Jimillar kudaden badakalar Abacha da aka kwato kawo yanzu = $3.624 billion.

Asali: Legit.ng

Online view pixel