Karin Bayani: Jami'ar yan sanda ce gurnet ya fadi daga hannunta, ba yar kunar bakin wake bace, NPF

Karin Bayani: Jami'ar yan sanda ce gurnet ya fadi daga hannunta, ba yar kunar bakin wake bace, NPF

- Tashin gurnet ya tada hankulan mutane a garin Afikpo na jihar Ebonyi

- Da farko an yi tunanin harin kunar bakin wake ne

- Hukumar yan sanda ta yi fashin baki kan ainihin abinda ya faru

Wani abin tashi tamkar Bam ya hallaka wata mata da akayi zargin yar kunar bakin wake ce a ranar Talata, 25 ga watan Mayu, 2021.

Wannan abu ya faru ne a garin Afikpo, karamar hukumar Afikpo na jihar Ebonyi.

Majiyar TheNation tace wannan abu ya faru ne misalin karfe 12 na rana.

"Yayinda tayi yunkurin shiga makarantar firamaren Amaizu/Amangballa amma masu gadi suka hanata shiga tunda ya gaza bayyana dalilinsa. Kawai sai ya garzaya cikin daji kuma aka ji tashin Bam," majiyar tace.

Majiyar ta kara da cewa mutane sun gudu yayinda suka ji tashin Bam.

Yayinda suka koma suka tarar da gawarta a kasa.

KARANTA NAN: Babban Limamim jami'ar UNIMAID zai aurar 'yayansa 10 rana guda

Yanzu haka: Dan kunar bakin wake ya tayar da Bam a jihar Ebonyi
Yanzu haka: Dan kunar bakin wake ya tayar da Bam a jihar Ebonyi
Asali: Original

DUBA NAN: Garba Shehu ya sani cewa shi fa kawai dan aike ne, yayi hattara da kalamansa: Gwamnonin kudu 17

Amma kakakin hukumar yan sandan jihar Ebonyi, Loveth Odah, ta bayyana cewa ba dan kunan bakin wake bane, wata jami'ar hukumar ce gurnet yayi kuskuren fadi daga hannunta kuma haka yayi sanadiyar tashin.

Kakakin ta ce sunan jami'ar Idi Aminu, kuma an garzaya da ita asibiti amma ta riga ta mutu, rahoton ChannelsTV.

A bangare guda, Tsagerun yan bindiga da ake zargin matasan IPOS/ESN ne sun shiga artabu da jami'an runduna ta musamman watau 'Special Forces' bayan bankawa ofishin yan sandan Orji, dake Owerri, wuta.

Misalin karfe 12 na rana, yan bindiga sun dira unguwar Orji dake birnin jihar kuma suka bankawa ofishin yan sanda wuta.

A riwayar Punch, harsashi ya bugi wata mata sakamakon wannan artabu da yan bindigan keyi da jami'an tsaro.

Matar ta kasance mai sayar da kaya a kusa da inda ake artabun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel