Yan bindiga sun bindige direban Sarkin Birnin-Gwari, Zubairu Jibrin Maigwari

Yan bindiga sun bindige direban Sarkin Birnin-Gwari, Zubairu Jibrin Maigwari

- Karo na biyu, yan bindiga sun kai wa motar Sarkin Birnin gwari hari

- Kamar na farko, Mai Martaba Zubairu Maigwari ba ya cikin motar

- Direban da dake tuka motar ne yayi rashin rayuwarsa

Tsagerun yan bindiga a ranar Asabar sun hallaka daya daga cikin direbobin Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibrin Maigwari II a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Daily Trust ta rahoto cewa bayan kashe direban mai suna Nasiru Sarkin Zango, yan bindiga sun bankawa motar fada kirar Toyota Hilux wuta.

An tattaro cewa wannan hari ya auku ne misalin karfe 3 na ranar yayinda direban ke hanyarsa ta komawa Birnin-Gwari daga Kaduna bayan gyaran motar.

Rahoton ya kara da cewa majiyoyi daga cikin fada sun bayyana cewa Nasiru Sarkin Zango kadai ke cikin motan lokacin da aka kai hari.

Hakazalika yan bindiga sun kai harin ne wajen dajin Unguwan Yako, daidai inda aka kaiwa ayarin motocin sarkin hari a watan Maris amma ba ya ciki lokaci

Wata majiya ta bayyana cewa an tafi da gawar mamacin cikin garin Birnin Gwari don jana'iza

Kakakin hukumar yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya tabbatar da lamarin.

DUBA NAN: An gudanar da Sallar Jana'izar Janar Ibrahim Attahiru da sauran Soji 5 da suka mutu

Yan bindiga sun bindige direban Sarkin Birnin-Gwari, Zubairu Jibrin Maigwari
Yan bindiga sun bindige direban Sarkin Birnin-Gwari, Zubairu Jibrin Maigwari
Asali: Original

DUBA NAN: Akalla sau 6 ya zo Borno, ya lashi takobin kawar da Boko Haram: Zulum ya yi jimamin rashin Attahiru

Wani mazaunin Birnin Gwari, Datti AbdulRauf ya bayyanawa Legit Hausa cewa: "Gaskiyane har anyi janazarsa bayan magrib muka dawo daga rakiyarsa a maqabarta. Ya Allah duk Masu siyasantar da matsalar tsaron bg Allah kahadasu da mummunan ajali."

Wani mazaunin Al-Abbas Umar yace: "Wannan yau yafaru, bayan magrib muka dawo rakiyarsa makabarta. Sai dai 2nd driver dins ane ba wancan da aka kaima hari na farko bane."

Asali: Legit.ng

Online view pixel