Yanzu-yanzu: An gudanar da Sallar Jana'izar Janar Ibrahim Attahiru da sauran Soji 5 da suka mutu
An gudanar Sallar Jana'iza ga manyan jami'an sojin Najeriya da suka mutu sakamakon hadarin jirgi ranar Juma'a, 21 ga watan Mayu, 2021 a babbar filin jirgin saman jihar Kaduna.
Daga cikin wadanda suka mutu akwai shugaban sojojin kasan Najeriya, Laftanan Janar Ibrahim Attahiru.
Daga cikinsu akwai mabiya addinin Islama shida da mabiya addinin Kirista 5.
Yayinda aka kai gawawwakin mabiya addinin Islaman babban masallacin brnin tarayya Abuja, an garzaya da na mabiya addinin Kiristan babban cocin hedkwatar hukumar Sojin sama.
An gudanar da Sallar Jana'izar ne misalin karfe 1:30 na rana.
Ga jerin wadanda akayiwa Sallar a babban Masallacin Abuja kamar yadda bidiyon Sallar jana'izar na Daily Trust ya nuna.
1. Laftanan Janar Ibrahim Attahiru
2. Birgediya Janar M I AbdulKadir
3. Birgediya Janar Kuliya
4. Manjo LA Hayatu
5 Manjo Hamza
6. Sajen Umar
KU KARANTA: Akalla sau 6 ya zo Borno, ya lashi takobin kawar da Boko Haram: Zulum ya yi jimamin rashin Attahiru
KU KARANTA: Jami'an tsaro sun kashe yan bindiga 7 da suka kashe 'dan Sarkin Kontagora, Bashir Namaska
Daga cikin wadanda suka halarci jana'izar akwai shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa'ad.
Hakazalika akwai Sifeto Janar na yan sanda, Mohammad Alkali; shugaban hukumar shiga da fice, Mohammed Babandede; Ministan tsaro, Bashir Salihi Magashi; da Ministan Sadarwa, Dr Isa Ali Pantami.
Sauran sune gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum; gwamnan Yobe, Mai Mala Buni; Sanata Kashim Shettima; Sanata Abubakar Kyari; dss.
Asali: Legit.ng