Akalla sau 6 ya zo Borno, ya lashi takobin kawar da Boko Haram: Zulum ya yi jimamin rashin Attahiru

Akalla sau 6 ya zo Borno, ya lashi takobin kawar da Boko Haram: Zulum ya yi jimamin rashin Attahiru

- Zulum, Shettima, Kyari sun halarci taron jana'izar hafsoshin sojin Najeriya da suka mutu

- Gwamnan Borno ya aike da sakon ta'aziyyarsa ga iyalan mamatan

- A cewarsa, za'ayi rashin Janar Attahiru saboda ya zage dantse waje kawar da Boko Haram

Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum tare da Sanatocin dake wakiltan Borno a majalisar dattawa, Kashim da Abubakar Kyari sun halarci Sallar Jana'izar marigayi shugaban kafsan sojin Najeriya, Laftanan Janar Ibrahim Attahiru.

Zulum ya bayyana cewa tun lokacin da aka nada Attahiru watanni hudu da suka gabata, ya ziyarci jihar Borno akalla sau shida domin ganin yadda lamura ke gudana wajen yaki da Boko Haram.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a jawabin ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin da yan Najeriya gaba daya.

Ya ce lallai ya bayyana karara marigayin ya zage dantse wajen ganin an kawar da yan ta'addan Boko Haram kuma ya lashi takobin yin hakan.

KU KARANTA: An gudanar da Sallar Jana'izar Janar Ibrahim Attahiru da sauran Soji 5 da suka mutu

Akalla sau 6 ya zo Borno, ya lashi takobin kawar da Boko Haram: Zulum ya yi jimamin rashin Attahiru
Akalla sau 6 ya zo Borno, ya lashi takobin kawar da Boko Haram: Zulum ya yi jimamin rashin Attahiru Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

DUBA NAN: Jami'an tsaro sun kashe yan bindiga 7 da suka kashe 'dan Sarkin Kontagora, Bashir Namaska

"Irin mayar da hankalin da marigayi tsohon babban hafsan sojin ya nuna wajen yaki da Boko Haram ya bayyana karara," Zulum yace.

"Cikin kankanin lokaci da yayi, ya ziyarci Borno sau tari, ya gana da kwamandoji da dakarun da ke faggen fama. Mutan Borno na godiya garesa da sauran jarumomin da suka mutu."

An gudanar Sallar Jana'iza ga manyan jami'an sojin Najeriya da suka mutu sakamakon hadarin jirgi ranar Juma'a, 21 ga watan Mayu, 2021 a babbar filin jirgin saman jihar Kaduna.

Daga cikin wadanda suka mutu akwai shugaban sojojin kasan Najeriya, Laftanan Janar Ibrahim Attahiru. Daga cikinsu akwai mabiya addinin Islama shida da mabiya addinin Kirista 5.

Asali: Legit.ng

Online view pixel