Uwargida ta hallaka mijinta don ya yiwa wata budurwa ciki

Uwargida ta hallaka mijinta don ya yiwa wata budurwa ciki

- Kishi ya ingiza wata mata kashe mijinta na aure a jihar Ogun

- Jami'an yan sanda sun samu nasarar damketa bayan ta gudu

- Matar da mijinta da ta kashe mahauta ne a garin Ijebu-Ode

Hukumar yan sanda a jihar Ogun ta damke wata mata mai suna Olanshile Nasirudeen, kan laifin dabawa mijinta wuka har lahira kan zargin ya yiwa wata mata ciki.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana hakan ga manema labarai, rahoton Premium Times.

Marigayin mai suna, Jimoh Nasirudeen, ya kasance mahauci kuma tare da matarsa yake aikin fawa a Ijebu-Ode.

Kakakin yan sandan ya ce Olanshile ce mata ta hudu a hannun marigayin.

A jawabin da hukumar ta saki, tace: "An damke matar ne bayan kiran da DPO na Obalende dake Ijebu-Ode ya samu cewa matar ta ga wacce mijinta ya yiwa ciki kuma ta fara tuhumarta kan shin ta wani dalili za ta bari mijinta yayi mata ciki."

Hukumar tace daga nan aka fara mujadala tsakanin matar da mijinta.

"Kawai sai ta dauki wuka ta bugawa marigayin a bayansa, kuma hakan yayi sanadiyar tsinkewar jijiyarsa. Da wuri aka kaishi asibiti kuma daga baya aka garzaya da shi asibitin General na Ijebu Ode inda ya yi numfashinsa na karshe saboda zubar jini," Kakakin yan sandan ya kara.

DUBA NAN: Babbar Magana: Mata Masu Juna Biyu 302,950 Suke Mutuwa Duk Shekara a Najeriya, Inji FG

Uwargida ta hallaka mijinta don ya yiwa wata budurwa ciki
Uwargida ta hallaka mijinta don ya yiwa wata budurwa ciki Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

DUBA NAN: Kungiyar Kwadago ta ba Gwamna El-Rufai awanni 48 ya dawo da wadanda aka kora daga aiki

Bayan haka matar ta gudu amma aka damke ta a unguwar Mobalufon da ta boye, cewar yan sanda.

"Yayin bincike, matar wacce take Amaryar ga marigayin ta ce mijinta ne ya fara faska mata mari saboda kawai ta kalubalanci matar da ya yiwa ciki."

A riwayar DailyPost, Mr Oyeyemi ya ce an mikawa iyalan mamacin gawar mutumin domin jana'izarsa bisa addinin Musulunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel