Babbar Magana: Mata Masu Juna Biyu 302,950 Suke Mutuwa Duk Shekara a Najeriya, Inji FG

Babbar Magana: Mata Masu Juna Biyu 302,950 Suke Mutuwa Duk Shekara a Najeriya, Inji FG

- FG tace mata masu juna biyu aƙalla 830 suke mutuwa a duk rana ta sanadiyyar wani abu da ya danganci juna biyu ko wajen haihuwa

- Ministan lafiya na ƙasa, Dr. Osagie Ehanire, shine ya bayyana haka a wani taron ƙarawa juna sani da aka shirya kan binciken lafiyar mata masu juna biyu

- Yace ya zama wajibi Najeriya ta miƙe tsaye wajen yin aiki tuƙuru ta kare lafiyar mata da ƙananan yara

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ana samun mata masu juna biyu 830 dake mutuwa wurin haihuwa kullum a Najeriya, jimulla 302,950 a shekara, kamar yadda thisday live ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Malami Ya Gargaɗi Gwmnonin Kudu a Kan Matakin Su Na Hana Makiyaya Kiwo

Wanna ƙiddigar na cikin jawabin ministan lafiya na ƙasa, Dr. Osagie Ehanire, a wajen taron ƙarawa juna sani da kuma bada shawarwari a a kan bincike da aka gudanar na lafiyar mata masu juna biyu da ƙananan yara a yankin Africa.

Babbar Magana: Mata Masu Juna Biyu 302,950 Suke Mutuwa Duk Shekara a Najeriya, Inji FG
Babbar Magana: Mata Masu Juna Biyu 302,950 Suke Mutuwa Duk Shekara a Najeriya, Inji FG Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Ohanire, wanda daraktan lafiya da ƙididdiga a ma'aikatar lafiya, Dr. Ngozi Anazodo, ta wakilta, yace:

"Najeriya da take da kashi ɗaya cikin ɗari na yawan al'ummar duniya, amma ita keda 13% na mace-macen mata masu juna biyu da jarirai yan ƙasa da shekara biyar a duniya."

KARANTA ANAN: El-Rufai: Ƙarɓar Haraji Daga Yan Najeriya Ne Zai Iya Farfado da Tattalin Arziki Ba Kudin Man Fetur Ba

"A kowace rana a Najeriya ana samun mata 830 dake mutuwa ta sanadiyyar wasu cututtuka dake da alaƙa da juna biyu ko wajen haihuwa."

"A duk mace ɗaya data mutu wajen haihuwa, to za'a samu wasu da dama da suka ji mummunan rauni ko wasu cututtuka a wajen haihuwan."

Ministan ya ƙara da cewa gudanar da bincike da kuma ɗaukar matakan da ya kamata shine zai rage yawan waɗannan mace-macen wurin haihuwa a ƙasar.

Yace aikin ƙara wayar da kan mata su fahimci muhimmancin zuwa duba lafiyar su zai sa a ɗauki dogon lokaci kafin rage yawan mutuwar mata da ƙananan yara a Najeriya.

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ƙara azama wajen inganta lafiyar ƙananan yara da jarirai, hakanne kaɗai cigaban da aka samu zuwa yanzun.

A wani labarin kuma Ahmad Lawan Ya Caccaki Masu Sukar Majalisa, Ya Nemi Yan Najeriya Su Musu Adalci

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda wasu ke sukar majalisa babtare da sanin ayyukanta ba, kamr yadda Dailytrust ta ruwaito.

Sanatan yace kamata yayi masu sukar majalisar dokoki su duba ayyukan da sukayi su soke su akansu ba wai da ra'ayi ba kawai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel