Kungiyar Kwadago ta ba Gwamna El-Rufai awanni 48 ya dawo da wadanda aka kora daga aiki

Kungiyar Kwadago ta ba Gwamna El-Rufai awanni 48 ya dawo da wadanda aka kora daga aiki

- Akwai yiwuwar cewa rashin jituwa tsakanin Gwamna El-Rufai da ma'aikatan lafiya na iya rikicewa

- Ma’aikatan kiwon lafiya sun nuna damuwa kan zargin da ake yi wa gwamnan na yakar ayyukan kwadago

- Ba a jima ba da kungiyar kwadago NLC ta dakatar da yajin aikin gargadi a jihar Kaduna

Rikicin masana'antu a jihar Kaduna ya ci gaba yayin da Kungiyar Likitoci da Ma'aikatan Lafiya ta Najeriya (MHWUN) ta ba wa gwamna Nasir El-Rufai wa'adin awanni 48, inda ta umarce shi da ya dawo da ma'aikatan jinya da aka kora wadanda ke kasa da mataki na 14.

Gwamnan na Kaduna ya ba da umarnin korar wasu ma’aikatan jinya da ba su je aiki ba ko kuma suka shiga yajin aikin gargadi na kungiyar kwadagon Najeriya (NLC) a jihar.

KU KARANTA KUMA: Ahmed Musa na shirin barin Kano Pillars a watan Yuni, ya yi jinjina ta musamman ga Ali Rabiu

Kungiyar Kwadago ta ba Gwamna El-Rufai awanni 48 ya dawo da wadanda aka kora daga aiki
Kungiyar Kwadago ta ba Gwamna El-Rufai awanni 48 ya dawo da wadanda aka kora daga aiki Hoto: @NLCHeadquarters, @GovKaduna
Asali: Twitter

Sai dai kuma, kungiyar ta MHWUN a cikin wata sanarwa daga shugaban ta, Biobelemoye Joy Josiah, ta soki gwamnan kan korar ma'aikatan lafiyar, Daily Trust ta ruwaito.

Kungiyar kwadagon ta ce baya ga dawo da ma’aikatan jinyan da aka kora, ya kamata El-Rufai ya nemi gafarar ma’aikatan Najeriya kan abubuwan da ya yi.

Kungiyar ta yi nuni da cewa korar ma’aikatan jinyar karya dokar kasa ne kuma rana ce ta bakin ciki ga dimokiradiyya.

MHWUN ta bayyana cewa zata iya ɗaukar mataki tare da haɗin kan korarrun ma'aikatan.

KU KARANTA KUMA: Hoton jarumin Kannywood Ali Nuhu tare da kyawawan yaransa

Sanarwar ta ce:

"A halin yanzu, muna kira ga mambobinmu a duk fadin kasar da su kasance a ankare kuma su jira ƙarin umarni kan wannan batun saboda raunata mutum ɗaya tamkar raunata kowa ne kuma rashin adalci a ko'ina rashin adalci ne a ko'ina.”

A gefe guda, mun ji cewa NLC ta dakatar da yajin aikin gargadi na kwanaki 5 a Kaduna, Shugaban NLC, Ayuba Wabba ya sanar da shawarar, ya ce ya yi hakan ne don girmama gayyatar da FG ta yi don sasanta rikicin da ke tsakanin kungiyar kwadagon da gwamnatin jihar Kaduna, in ji TVC.

Channels Tv ta ruwaito cewa, a safiyar yau, Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige ya shiga cikin takun-saka tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da kungiyoyin kwadago ta hanyar gayyatar bangarorin biyu zuwa taron sasantawa.

Ngige ya umarci bangarorin biyu da su ci gaba da kasancewa a yadda suke har zuwa lokacin da za a sasanta batutuwan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel