Kelechi Iheanacho da Taurarin Super Eagles 5 da su ka yi abin da babu wanda ya taba yi a Ingila

Kelechi Iheanacho da Taurarin Super Eagles 5 da su ka yi abin da babu wanda ya taba yi a Ingila

A ranar Talata ‘dan wasan Leicester City, Kelechi Iheanacho ya zura kwallo a gwabzawarsu da Chelsea a wasan daf da karshe a gasar Firimiyan bana.

ESPN ta ce ‘dan wasan gaban kungiyar Leicester City ya kafa tarihi a wannan dare, inda ya zama ‘dan wasan da ya taba cin kwallo a kowane ranar mako.

Daga ranar Litinin zuwa Lahadi, babu ranar da Kelechi Iheanacho bai taba cin kwallo ba. Tun da ake buga gasar BPL, ba a samu wanda ya yi wannan ba.

Goal.com ta tattaro jerin ‘yan wasan Najeriya da suka bar tarihi a gasar Firimiya na kasar Ingila.

1. Kelechi Iheanacho

‘Dan wasa Kelechi Iheanacho shi ne wanda ya taba cin kwallo a ranar Litinin, Talata, Laraba, Alhamis, Juma’a, Asabar da Lahadi a kakar shekara guda.

KU KARANTA: Ahmed Musa ya bada gudummawar N2m a gina masallaci

2. Victor Anichebe

Ya na shekara 18 rak a Duniya, ‘dan wasa Victor Anichebe ya zura kwallo a raga. ‘Dan wasan Najeriyan ya yi wannan ne a 2006 da kungiyar Everton.

3. Efan Ekoku

Effan Ekoku shi ne ‘dan kwallon Najeriya na farko a tarihi da ya fara cin kwallo a gasar Firimiya. Ekoku ya bar wannan tarihi ne a Bournemouth tun 1993.

4. Victor Moses

Tauraron Super Eagles da ya fi kowa cin kwallaye da kungiyoyi daban-dabam shi ne Victor Moses. ‘Dan wasan ya ci kwallaye 20 da kungiyoyin Ingila biyar.

Moses ya bugawa Wigan Athletic, Chelsea, Liverpool, Stoke City da kungiyar West Ham United.

KU KARANTA: 'Dan wasa Ahmad Musa ya nuna hotunan wasu motocinsa

Kelechi Iheanacho da Taurarin Super Eagles 5 da su ka yi abin da babu wanda ya taba yi a Ingila
Nwankwo Kanu, Kelechi Iheanacho da Yakubu Ayegbeni Hoto: www.goal.com
Asali: UGC

5. Yakubu Ayegbeni

A cikin ‘Yan wasan Afrika da suka yi kwallo a Firimiya, babu wanda ya fi Yakubu Ayegbeni zura kwallaye uku a wasa guda, Tauraron ya yi wannan sau hudu.

6. Nwankwo Kanu

A tarihin gasar BPL, babu Tauraron Afrikan da ya zarce tsohon ‘dan wasan Arsenal, Nwankwo Kanu, wajen taimakawa a ci kwallo, ya bada kwallaye 29 da aka ci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel