Ahmed Musa ya bada gudummawar Naira miliyan 2 ga makarantar soja domin aikin masallaci

Ahmed Musa ya bada gudummawar Naira miliyan 2 ga makarantar soja domin aikin masallaci

- Dan wasan kwallon kafa, Ahmed Musa ya bayar da gudummawar naira miliyan biyu ga makarantar sakandare ta sojoji ta Bukavu da ke Kano don gina masallaci

- Har ila yau kyaftin din na Super Eagles ya yi alkawarin samar da kujeru a azuzuwan makarantun wadanda suka yi karanci

- Musa ya kuma yi nasiha ga daliban a kan su guji shan kwayoyi da sauran munanan halaye, idan suna son su zama mutane masu fa'ida cikin al’umma

Sabon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Ahmed Musa a jiya Alhamis, ya bayar da gudummawar naira miliyan biyu ga makarantar sakandare ta sojoji ta Bukavu da ke Kano don gina masallaci.

Kyaftin din na Super Eagles ya bayar da gudummawar ne lokacin da ya ziyarci makarantar bayan kammala atisayen ranar Alhamis.

Ya kuma yi alkawarin samar da kayan kujeru a wasu daga cikin azuzuwan domin magance matsalar karancin kujeru.

Ahmed Musa ya bada gudummawar Naira miliyan 2 ga makarantar soja domin aikin masallaci
Ahmed Musa ya bada gudummawar Naira miliyan 2 ga makarantar soja domin aikin masallaci Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga: Matawalle ya koka, ya ba da umarnin rufe kasuwannin Zamfara 4 nan take

Da yake jawabi ga daliban, Ahmed Musa ya umarce su da su mai da hankali ga karatunsu don samun nasara a rayuwa.

Bugu da ƙari, ya umurce su da su guji shan kwayoyi da sauran munanan halaye, idan suna son su zama mutane masu fa'ida cikin al’umma.

Yayin da yake bayyana kudurinsa na bunkasa ilimin addinin Musulunci da na boko, Musa ya godewa malamai kan baiwa daliban ilimi mai inganci.

A nasa jawabin, Daraktan makarantar, Alhaji Yusuf Saidu ya godewa tsohon dan wasan na CSKA Moscow da kungiyar kwallon kafa ta Leceister City bisa ziyarar da ya kawo masa tare da yi masa fatan Allah ya yi masa jagora a kan aikin nasa.

Kafin 'yan wasan su nuna alama, Daraktan ya lissafa wasu matsalolin da makarantar ke fuskanta wadanda suka hada da rashin masallaci, bandakuna da kayan daki a wasu aji.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Fadar shugaban kasa ta bayyana goyon bayanta ga Pantami

A wani labarin, Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya kammala cibiyarsa ta wasanni ta miliyoyin naira a Kaduna inda ake sa ran matasa za su samu horo kuma za su iya baje kolin baiwarsu ma.

Tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Leceister City yana daya daga cikin attajiran yan wasan Najeriya idan aka yi la’akari da kadarorin sa tun lokacin da ya fara wasan kwallon kafa daga titin garin Jos.

Ahmed Musa ya fara wasan kwallon kafa a garin Jos kafin ya koma kungiyar JUTH FC daga inda tsohon zakaran gasar kwallon kafa ta Kano Pillars ya sanya masa hannu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel