Yanzu-Yanzu: El-Rufai Ya Kori Dukkan Ma'aikatan Jinya Masu Mataki Na 14 Zuwa Ƙasa

Yanzu-Yanzu: El-Rufai Ya Kori Dukkan Ma'aikatan Jinya Masu Mataki Na 14 Zuwa Ƙasa

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya sallami dukkan ma'aikatan jinya da ke asibitocin jihar daga mataki na 14 zuwa kasa saboda shiga yajin aiki na kungiyar ƙwadago NLC, The Punch ta ruwaito.

Gwamnan ya umurci ma'aikatan lafiya na jihar ta fitar da sanarwar guraben aiki nan take domin neman wadanda za su maye guraben su.

DUBA WANNAN: Yakin Aiki: Gwamna El-Rufai Ya Gaza Kama Wabba a Kaduna

Yajin Aiki: El-Rufai Ya Kori Dukkan Ma'aikatan Jinya Masu Mataki Na 14 Zuwa Ƙasa
Yajin Aiki: El-Rufai Ya Kori Dukkan Ma'aikatan Jinya Masu Mataki Na 14 Zuwa Ƙasa. Hoto: @MobilePunch
Asali: Facebook

An tsayar da ayyuka a jihar Kaduna tsawon awa 48 da suka gabata saboda yakin aikin da aka fara inda ma'aikata da dama suka shiga kan abin da suka kira rashin adalci gwamnatin El-Rufai na korar ma'aikata fiye da 60,000.

Amma sanarwar da gwamnan ya fitar a ranar Talata ta kira yajin aikin laifi da sunan zanga-zanga.

DUBA WANNAN: Dattawan Arewa Sun Goyi Bayan Gwamnonin Kudu, Sun Ce Dole a Dena Kiwo a Fili

A sanarwar da mashawarcin gwamnan Muyiwa Adeleke ya fitar, El-Rufai ya gargadi cewa duk wani ma'aikacin da ba a same shi a wurin aiki ba zai rasa aikinsa.

Ku saurari ƙarin bayani ...

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Raya Birnin Tarayya Abuja, FCTA, ta rushe wani tashar tasi a NICON Junction, Maitama, Abuja, kan zargin mayar da tashar matattarar yan kwaya da bata gari, Daily Trust ta ruwaito.

Direktan (FCTA), sashin tsaro, Adamu Gwari, wanda ya yi magana yayin rushe tashar ya ce tashar barazanar tsaro ne sannan barazana ne ga muhallin mutanen da ke zaune a birnin. An Rushe Tashar Motar Saboda Ta Zama 'Matattarar Ƴan Ƙwaya' a Abuja.

Ya kuma ce rushe tashar mataki ne da aka dauka duba da irin kallubalen tsaron da ake fuskanta a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel