Dattawan Arewa Sun Goyi Bayan Gwamnonin Kudu, Sun Ce Dole a Dena Kiwo a Fili

Dattawan Arewa Sun Goyi Bayan Gwamnonin Kudu, Sun Ce Dole a Dena Kiwo a Fili

- Kungiyar Dattawan Arewacin Nigeria, ACF, ta ce tana goyon bayan matakin gwamnonin kudu na hana kiwo a yankinsu

- ACF ɗin ta ce gwamnonin sun dauki matakin ne domin kare manoma da abin da suke nomawa hakan kuma na da tasiri wurin ciyar da kasa

- Kazalika, ACF ta shawarci gwamnonin jihohin arewa su yi koyi da gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje su samar da wuraren kiwo na musamman

Kungiyar Dattawan Arewacin Nigeria, ACF, a jiya Litinin, ta goyi bayan matakin da gwamnonin kudu suka ɗauka na hana kiwo a fili a jihohinsu 17, Daily Trust ta ruwaito.

ACF ɗin, cikin sanarwar da shugaban ta Cif Audu Ogbeh ya fitar ta ce ta amince da matakin domin an yi hakan ne don kiyaye kayan amfanin manoma.

ACF ta goyi bayan gwamnonin kudu, ta ce dole a dena kiwo a fili
ACF ta goyi bayan gwamnonin kudu, ta ce dole a dena kiwo a fili. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Falaɗinawa Sun Harbo Mana Roka 3,150 Daga Gaza, Isra'ila

Ogbeh ya ce, "Maganan gaskiya shine rikicin ya samo asali ne saboda mafi yawancin makiyaya sunyi imanin cewa sun da damar shiga kowanne gona su yi kiwo, su yi fyaɗe ko kashe duk wani da ya nemi hana su. Babu wanda zai amince da hakan.

"Tashin gwauron zabi da farashin garri ya yi a yanzu na ɗaya daga cikin abubuwan da hakan ya haifar. Gonaki ƙalilan ne suka shuka rogo kuma su kan cire kafin ya ƙosa. Don haka akwai barazanar ƙarancin abinci."

Ya kuma yi kira ga gwamnonin da kada su yi ƙasa a gwiwa kan matakin da suka ɗauka na hana kiwo a filin yana mai cewa, 'wasu ƴan kasashen waje suna shigowa Nigeria ba bisa ka'ida ba. Ya kuma kamata a dakatar da su.'

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Ƴan Bindiga Sun Sace Farfesa Da Mijinta a Gidansu

Ya kuma ce a ɗauki irin matakin da gwamnan Abdullahi Ganduje na Kano ya ɗauka don hana shigowar shanu daga ƙasashen Afirka ta Yamma sannan Nigeria ta nemi a yi wa dokar Article 3 na Ecowas kwaskwarima musamman ɓangaren da ya shafi zirga-zirgan dabbobi ba tare da samun izini na musamman ba.

"Idan mun yi hakan, muna da fiye da hekta miliyan 5 na filin kiwo da zai wadatar da shanu miliyan 40 idan an kula da shi".

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Raya Birnin Tarayya Abuja, FCTA, ta rushe wani tashar tasi a NICON Junction, Maitama, Abuja, kan zargin mayar da tashar matattarar yan kwaya da bata gari, Daily Trust ta ruwaito.

Direktan (FCTA), sashin tsaro, Adamu Gwari, wanda ya yi magana yayin rushe tashar ya ce tashar barazanar tsaro ne sannan barazana ne ga muhallin mutanen da ke zaune a birnin. An Rushe Tashar Motar Saboda Ta Zama 'Matattarar Ƴan Ƙwaya' a Abuja.

Ya kuma ce rushe tashar mataki ne da aka dauka duba da irin kallubalen tsaron da ake fuskanta a jihar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel