Matan da su ka fara rike mukaman Ministoci da Jakadu a tarihin Gwamnatin Tarayya

Matan da su ka fara rike mukaman Ministoci da Jakadu a tarihin Gwamnatin Tarayya

- Shehu Shagari ne ya fara tafiya da mata da matasa a Gwamatinsa a 1978

- A gwamnatin Shagari ne irinsu Ebun Oyagbola suka fara rike mukamai

A Najeriya da mafi yawan sauran kasashen nahiyar Afrika, ana kukan ba a yi da mata wajen sha’anin tafiyar da gwamnati da harkar siyasa.

Wannan karo mun kawo maku wasu fitattun mata wanda suka fara shiga gwamnatin tarayya.

Tsohon shugaban kasa, Marigayi Alhaji Shehu Usman Shagari, shi ne ya jawo wadannan mata a cikin gwamnatinsa da ya yi tsakanin 1979 da 1984.

KU KARANTA: Takaitaccen tarihin Alhaji Shehu Shagari

Alhaji Shehu Shagari ne ya bada umarnin cewa a rika ba mata da matasa mukamai a kowace jiha. Asali ma ya so mace ne ta zama mataimakiyarsa.

1. Ebun Oyagbola

Gwamnatin Shehu Shagri ta nada Ebun Oyagbola a matsayin Ministar tsare-tsaren tattali da kasafi. Daga baya ta zama Jakada zuwa kasashen Amurka.

2. Janet Akinrinade

Har ila yau, gwamnatin farar hular da aka kafa a Oktoban shekarar 1984, ta zabi Janet Akinrinade a matsayin karamar Ministar harkokin cikin gida.

KU KARANTA: An yanke wutar gidan tsohon shugaban ƙasa, Shagari

Matan da su ka fara rike mukaman Ministoci da Jakadu a tarihin Gwamnatin Tarayya
Alh. Shehu Shagari Hoto: www.guardian.ng
Asali: UGC

3. Elizabeth Ogbon

Elizabeth Ogbon ta yi aiki da ofishin Jakadancin Najeriya zuwa kasar Jamus da ke birnin Hamburg. Ita ce macen da ta fara zama Jakada, ta rasu a 2014.

4. R Mohammed

Bayan Elizabeth Ogbon ta shara fage, R. Mohammed ta hau kujerar Jakadan Najeriya zuwa kasar Bostwana, daga baya ta zama Jakadar kasar Zimbabwe.

Bayan wadannan akwai wasu matan da su ka samu kujerar Ministocin tarayya a gwamnatin Shagari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel