An yanke wutar gidan tsohon shugaban ƙasa, Shehu Shagari saboda bashi

An yanke wutar gidan tsohon shugaban ƙasa, Shehu Shagari saboda bashi

- An yanke wutar gidan tsohon shugaban Najeriya Shehu Shagari bayan biyo shi tulin bashi da ya dara naira mililiyan 6

- Kamfanin rarraba lantarki na Jihar Kaduna KAEDCO ya bayyana cewa ba a biya kudin ba tun rasuwar Shagari a 2018

- Iyalan sa sun bayyana cewa tun rasuwar sa gwamnatin Sokoto ta dauki nauyin biyan kudin wutar gidan nashi

Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Jihar Kaduna, KAEDCO, a ranar Laraba, ya yanke wutar gidan marigayi Shehu Shagari, shugaban kasar Najeriya a jamhuriyya ta biyu, saboda bashin sama da miliyan 6.

Tsohon shugaban kasar ya rasu ranar 28 ga watan Disambar 2018, yana da shekaru 93.

Da ya ke tabbatar da lamarin yanke wutar a titin Sama, gidan tsohon shugaban da ke Sokoto, mai magana da yawun Kamfanin, Abdulaziz Abdullahi, ya ce ba a biya kudin wuta ba tun rasuwar Shagari.

Kamfanin lantarkin Kaduna ya yanke wutar gidan tsohon shugaban kasa
Kamfanin lantarkin Kaduna ya yanke wutar gidan tsohon shugaban kasa. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda matashi ya yi garkuwa da mahaifinsa ya karbi naira miliyan 2 kuɗin fansa

"Kamfanin ya ba su isashen lokaci don biyan kudaden kafin a yanke wutar," inji Abdullahi.

Wani daga cikin iyalan ya shaidawa Daily Star, wani gidan jaridar yanar gizo a Sokoto, tun rasuwar Shagari, gwamnatin Jihar ta soke biyan kudin wutar sa.

"Yan kwanaki kadan da suka wuce, jami'an KAEDCO suka kawo mana jadawalin wuta, kuma suka ce zasu yanke idan ba a biya kudin ba.

"Mun shaida musu cewa gwamnatin jihar ce ke biyan kudin, amma suka ce su bai shafe su ba," a cewar majiyar.

KU KARANTA: Wanda na fara sace wa shine tsohon saurayi na da ya ƙi aure na, in ji mai garkuwa, Maryam

Wani jami'in gwamnatin Jihar Sokoto wanda ya zanta da jaridar ya kuma bukaci a sakaye sunan shi, ya ce rashin adalci ne a zargi gwamnatin jiha ba ta tarayya ba.

"Kasan daukar nauyin iyalan tsohon shugaban kasa ya rataya ne a wuyan gwamnatin tarayya, idan gwamnatin jiha ta sa hannu, kawai kyautatawa ce da girmama marigayin," a cewar majiyar.

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel