Aljanu Biliyan 3 su ka karbi Darikar Tijjaniya a Duniya inji Sheikh Dahiru Bauchi
- Babban Malami Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce Aljanu biliyan uku su ka karbi Darikar Tijjaniya
- Babban Malamin ya ce daga cikin wadannan Aljanu, akwai mukaddamai miliyan dari biyu
- Akwai yiwuwar a rika amfani da Aljanun domin maganin masu garkuwa da mutane
Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi wata magana wanda ta ba dinbin mabiyansa da sauran al’umma mamaki.
Shehin malamin ya bayyana cewa akwai wasu kebantattun mutane da su ke iya sadu wa da aljanu. Ya ce ya na daga cikin masu mu’amala da su.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce wasu suna ganinsu, har su yi magana da su, kamar yadda shaidanun mutane su ke hulda da shaidanun Aljanu.
A cewar Sheikh Dahiru Usman Bauchi akwai Aljanu muminai, daga cikin su har mabiya Darikar Tijjaniya wanda yanzu adadinsu ya zarce biliyan uku.
Shehin darikar ya ke cewa daga cikinsu akwai mukaddamai miliyan 200 wadanda su ka yi nisa a Tijjaniya.
Duk da tulin wadannan dakarun Aljanu da suka karbi darikar Tijjaniya, shehin malamin ya ce ba za a rasa wasu dinbin mabiyan da ba a san da zamansu ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dattijon malamin yake cewa suna kokarin ganin an zakulo manyan malamai daga cikin Aljannun da aka ba Darikar Tijjaniya, da nufin yada addini.
“Mu na zama da su, amma babu wani alkawari da aka yi da su na yin abin da bai kamata ba.” "Mu ne mukaddamai a cikinsu" inji Shehi Dahiru Usman Bauchi.
Dahiru Usman Bauchi ya ke cewa an kawo shawarar ayi amfani da wadannan rundunar Aljanu domin ceto ‘Yan Tijjaniya daga hannun miyagu a Najeriya.
Ya ce: “Muna shawarar mu nemi alfarmar a yi amfani da su wajen maganin masu zagin Waliyyai, da satar mutane, da ‘yan bindiga da kuma ‘Yan Boko Haram.”
A karshen makon nan, kun ji cewa An zabi Dr. Isa Ali Pantami a matsayin Ministan tarayyar da ya yi fice a shekarar nan ta 2021, an kuma ba shi lambar yabo.
Shigo da tsarin rajistar NIN ya sa mujallar People and Power ta Dr. Isa Pantami ya zama Gwarzon Ministan shekara a lokacin da aka huro wuta ya ajiye aikinsa.
Asali: Legit.ng