Ana tsakar ce-ce-ku-cen ya yi murabus, Ministan sadarwa, Pantami ya lashe lambar yabo

Ana tsakar ce-ce-ku-cen ya yi murabus, Ministan sadarwa, Pantami ya lashe lambar yabo

- Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya zama gwarzon Ministan shekarar nan ta 2021

- Mujallar People and Power ce ta ba Ministan sadarwan wannan lambar yabo

- Hakan na zuwa ne lokacin da aka huro wa Pantami ya sauka daga kujerarsa

Mun samu labari cewa Mai girma Ministan sadarwa da bunkasa tattalin arzikin zamani na kasa, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya samu lambar yabo.

Isa Ali Ibrahim Pantami ya samu kyautar gwarzon Ministan Najeriya da ya yi fice a shekarar nan.

Kamar yadda rahotanni su ka tabbatar, mujallar nan ta People and Power ce ta ba Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamanin wannan lamba.

KU KARANTA: PDP ta hurowa Shugaba Buhari wuta, ya sallami Sheikh Pantami

A shafinta na sada zumunta na Facebook, Ma’aikatar sadarwa da bunkasa tattalin arzikin zamani ta tabbatar da wannan kyauta da Ministan ya samu.

Ma’aikatar tarayyar ta ce an zabi Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami, an ba shi wannan kyauta ne saboda irin tarin gudumuwar da manufofin ofishinsa su ka kawo.

Daga cikin abubuwan da su ka sa aka ba Ministan wannan lambar yabo da jinjina, akwai tsarin danganta lambar ‘dan kasa da layin wayar salula da ake yi.

Bayan haka, mujallar People and Power ta yaba da manufofin sadarwa na zamani da Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya shigo da su bayan ya shiga gwamnati.

Ana tsakar ce-ce-ku-cen ya yi murabus, Ministan sadarwa, Pantami ya lashe lambar yabo
Ministan sadarwa, Isa Pantami Hoto: www.facebook.com/21841736528663
Source: Twitter

KU KARANTA: Jami’an tsaro sun kama Mai tsafi da jikin mutane a jihar Kwara

Ba wannan ne karon farko da Isa Pantami ya lashe irin wannan kyauta ba, an yi irin haka a baya.

Mutane sun tofa albarkacin bakinsu game da wannan lambar yabo da aka ba Ministan, wasu suna ganin ya cancanci wannan karrama wa da aka yi masa.

A daidai wannan lokaci kuma wasu sun soki lamarin, inda suka cigaba da yin kira ga Ministan ya ajiye mukamin da yake kai saboda zargin da ake jifansa da su.

A baya kun ji Isa Pantami ya nesanta kansa da wasu kalamai da yayi a baya kan wasu ƙungiyoyin 'Yan ta'adda, ya ce tuni ya dawo daga rakiyar wannan ra'ayin.

Ministan yace ya warware tafkar da ya yi saboda ƙarin ilmi da gogewa. Dr. Isa Pantami, ya ce ya canza wasu daga cikin fatawoyinsa a kan Alƙa'ida da Taliban.

Source: Legit.ng

Online view pixel