Yanzu-Yanzu: Shugabannin Tsaro Na Ganawar Sirri Da 'Yan Majalisar Tarayya

Yanzu-Yanzu: Shugabannin Tsaro Na Ganawar Sirri Da 'Yan Majalisar Tarayya

- Shugabannin hukumomin tsaron Nigeria sun amsa gayyatar da majalisar dattijai ta yi musu

- Majalisar ta gayyaci shugabannin tsaron su bayyana gabanta ne kan halin rashin tsaro da kasar ke ciki

- Yan bindiga da yan ta'adda ne ke addabar yankin arewacin kasar yayin da yan daba ke kaiwa yan sanda da wasu hukumomin gwamnati hari a kudu

Shugabannin rundunar sojojin Nigeria sun bayyana gaban majalisar tarayya saboda kallubalen tsaro da ake fama da shi a kasar, The Cable ta ruwaito.

Wadanda suka halarci majalisar sun hada da Lucky Irabor, babban hafsan tsaro; Ibrahim Attahiru, babban hafsa sojojin kasa; Awwal Gambo, babban hafsan sojojin ruwa da Isiaka Amao, babban hafsan sojojin sama.

DUBA WANNAN: Jonathan Ya Yi Jinjina Ga Tsohon Mai Gidansa Ƴar’Adua Shekaru 11 Bayan Rasuwarsa

Yanzu-Yanzu: Shugabannin Hukumomin Tsaro Sun Bayyana Gaban Majalisar Tarayya
Yanzu-Yanzu: Shugabannin Hukumomin Tsaro Sun Bayyana Gaban Majalisar Tarayya. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Saura shugabannin hukumomin tsaro kamar hukumar tattara bayannan sirri na kasa, NIA, da Hukumar Yan sandan Farar Hula, DSS da Rundunar Yan sandan Nigeria suma sun hallarci taron.

Suna ganawa da yan majalisar tarayyar ne cikin sirri.

Majalisar ta gayyaci shugabannin hukumomin tsaron ne a makon da ya gabata biyo bayan mahawara kan kudin halin rashin tsaro da kasar ke ciki.

Mohammed Sani Musa, Sanata mai wakiltar Niger ta gabas, ya janyo hankalin takwarorinsa kan rahoton cewa kungiyar Boko Haram ta kafa tuta a karamar hukumar Shiroro na jihar Niger.

KU KARANTA: Gumi Ya Faɗa Mana Gaskiya, Yana Tare Da Ƴan Ta’adda Ne Ko Ƴan Nigeria, Adamu Garba

A ranar Talata ya kamata su bayyana a gaban majalisar amma aka dage zuwa Alhamis saboda taron majalisar tsaro na kasa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi irin wannan taron da shugabannin tsaron da nufin samar da mafita kan halin rashin tsaro a kasar.

A baya bayan nan ana samun karuwar garkuwa da mutane, harin yan bindiga da ta'addanci.

A arewa yan bindiga da yan ta'addan Boko Haram na addabar mutane yayin da jami'an tsaro da hukumomin gwamnati ake kai wa hari a kudancin kasar.

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel