PDP Za Ta Matsawa Buhari Lamba Ya Samar Da Tsaro a Nigeria, Saraki

PDP Za Ta Matsawa Buhari Lamba Ya Samar Da Tsaro a Nigeria, Saraki

- Sanata Bukola Saraki ya ce jam'iyyar PDP za ta cigaba da yi wa Buhari matsin lamba don ganin an samu tsaro a Nigeria

- Tsohon shugaban majalisar na dattawa ya ce za su rika amfani da hanyoyin da doka ta amince da su domin cimma wannan manufa

- Saraki ya shaidawa yan NIgeria cewa dauyi ne a kan kowanne dan Nigeria sanar da gwamnati idan ta gaza a wasu bangarori domin a gyara

Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa ya ce jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) za ta matsawa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari lamba domin ta ceto kasar daga rashin tsaro.

A jawabinsa yayin taron manema labarai a sakatariyar PDP na kasa a Abuja a ranar Litinin, Saraki ya ce jam'iyyar adawar za ta cigaba da bada shawarwari kan yadda za a warware kallubalen tsaro da wasu matsalolin da ke adabar kasar.

PDP Za Ta Matsawa Buhari Lamba Ya Samar Da Tsaro a Nigeria, Saraki
PDP Za Ta Matsawa Buhari Lamba Ya Samar Da Tsaro a Nigeria, Saraki. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda Muka Hana a Yi Wa Matasan Arewa 45 Kisar Gilla a Ondo, Amotekun

Tsohon shugaban majalisar dattawar ya ce - matsayin lamba ta hanyoyin da kundin tsari ta amince da su - za su samar da sakamakon da yan kasa ke bukata.

"Mu a jam'iyyar hamayya, za mu cigaba da taka rawar mu wurin ankarar da gwamnati kan a wuraren da ta gaza da cigaba da yi mata matsin lamba ta hanyar da doka ta amince da shi domin su yi abin da ya dace, don haka ba za mu gaji ba.

"Idan ka ga canji a duniya, ta kudin tsarin mulki aka samar da shi. Zai iya daukan lokaci mai tsawo amma gaskiya za ta fito kuma za a yi abin da ya kamata.

"Idan muna magana kan tsaro, ba batun jam'iyyar siyasa bane. Abu ne da ya shafi dukkan yan Nigeria. Wannan nauyin ya rataya ne a kan dukkan mu yan Nigeria, in ji shi.

A wani labarin daban kunji wasu matasa a Daura, a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.

Hon. Adam ya bada misali dokar 'Not Too Young To Run' da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam'iyyar PDP da wasu sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel