Yadda Muka Hana a Yi Wa Matasan Arewa 45 Kisar Gilla a Ondo, Amotekun

Yadda Muka Hana a Yi Wa Matasan Arewa 45 Kisar Gilla a Ondo, Amotekun

- Gwamnatin Jihar Ondo za ta mayar da matasa yan arewa 45 zuwa jihohin su

- Matasan wadda kungiyar tsaro ta Amotekun ta kama sun ce sun je daukar horo ne don aikin gadi

- Gwamnatin jihar ta yabawa jami'an tsaro kan irin bajintar da tayi wajen ganin tabbatuwar zaman lafiya a jihar

Gwamnatin Ondo tace tana kokarin tabbatar da cewa ta mayar da matasan arewa 45 da aka kama a karamar hukumar Okitipupa da ke jihar zuwa jihohinsu cikin koshin lafiya, The Cable ta ruwaito.

Jami'an kugiyar tsaro ta kudancin Najeriya, Amotekun, sune suka kama matasan ranar Alhamis.

Matasan wanda suka isa karamar hukumar a cikin babbar motar daukar kaya sun ce sun je garin ne don daukar horo a barikin sojoji don yin aikin gadi.

Yadda Muka Hana a Yi Wa Matasan Arewa 45 Kisar Gilla a Ondo, Amotekun
Yadda Muka Hana a Yi Wa Matasan Arewa 45 Kisar Gilla a Ondo, Amotekun. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jerry Gana Ya Yi Barazanar Maka Majalisar Ƙolin Musuluncin Nigeria a Kotu

Adetunji Adeleye, kwamandan Amotekun a jihar, ya ce yayin da ake tuhumar su, an gano cewa matasan wadda suka fito daga jihohin Kano da Jigawa, sun zo garin ne don samun aiki da wani karamin kamfani da ba a sani ba.

"Abun da suka fada, bamu gamsu da shi ba kuma da muka tsananta bincike, da yawa daga cikin su ba su san yadda akayi suka zo inda suke ba, kawai dai an fada musu za su je daukar horo," a cewar sa.

"A cikakken binciken da muka gudanar, mun gano wanda suka dauki nauyi kuma sun ce kungiya ce mai zaman kanta, NGO. Yanzu dai, muna kallon su a matsayin barazana ga tsaron jihar."

Da yake martani kan faruwar lamarin ranar Lahadi, Donald Ojogohe, kwamishanan sadarwa da wayar da kan al'umma, ya bayyana lamarin a matsayin "abun tsoro", ya ce lamarin na iya haddasa tashin hankali ba dan jami'an tsaro sunyi aiki da kwarewa ba.

"Yanayin da muka tsinci kan mu na tsaro cikin awanni 72 da suka shude abun tsoro ne kwarai da gaske. In banda jami'an gwamnati, musamman kwamandan Amotekun da mai bawa gwamna shawara kan harkokin tsaro sun nuna kwarewa, lamarin na iya janyo tashin hankali," a cewarsa.

KU KARANTA: Gwamna Zulum Ya Miƙa Gwamnatin Jihar Borno Ga Usman Kadafur

"Kokarin da gwamnati take yi a yanzu shine ta tabbatar yadda suka shigo jihar nan, sun fita lafiya, cikin lumana ba tare da an cutar da su ba, ta yadda in sun koma jihohinsu, za su bada shaida ga gwamnatocin jihohinsu cewa abun da ya kawo su jihar Ondo ba a gamsu da shi ba kuma gwamnatin jihar ta ba su kariya har sun dawo jiharsu."

Kwamishinan ya shawarci al'umma da su fara sanarwa jami'an tsaro idan wata matsala ta taso.

Ya ce "ina amfani da wannan damar wajen sanar daku cewa gwamna ya ce a sanar daku, musumman jami'an gwamnati, cewa duk wani sha'anin tsaro da muka tsinci kan mu, wanda zamu tuntuba dole su kasance jami'an tsaro."

A wani labarin daban kunji wasu matasa a Daura a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.

Hon. Adam ya bada misali dokar 'Not Too Young To Run' da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam'iyyar PDP da wasu sauransu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel