Ba mu da niyyar kara farashin wutan lantarki, Minista Saleh Mamman

Ba mu da niyyar kara farashin wutan lantarki, Minista Saleh Mamman

- Yan Najeriya su kwantar da hankalinsu, Minista Saleh Mamman ya bayyana

- An fara rade-radin shirin sake kara farashin wutan lantarki a watan nan

- Ministar Lantarki ya yi fashin baki kan lamarin

Ministan Lantarki, Injiniya Saleh Mamman, ya yi watsi da rahotannin cewa an shirin kara farashin wutar lantarki a Najeriya, inda ya ce basu da niyyar yin hakan.

A jawabin da ya saki a Abuja, Ministan ya bayyana cewa maimakon kara farashin wutan, za'a karawa yan Najeriya ingancin wutan lantarkin.

Wannan jawabi ya biyo bayan rahotannin cewa akwai yiwuwan kara farashin wutan kwanan nan sakamakon jawabin hukumar hukumar lura da lantarkin Najeriya NERC

Mamman ya ce jawabin da NERC ta saki ranar 26 ga Afrilu, abine da suka saba yi sau biyu a shekara.

A cewarsa, "har yanzu muna da bada tallafi ga yan band D&E (mutanen da ke samun wuta kasa da awanni 12 a rana) bisa ga umurnin gwamnatin tarayya."

Mamman ya ce gwamnatin tarayya na cika alkawuran da tayi da kungiyar kwadago.

KU KARANTA: A jihar Kano kadai ake yaki da rashawa kamar EFCC da ICPC, Gwamna Ganduje

Ba mu da niyyar kara farashin wutan lantarki, Minista Saleh Mamman
Ba mu da niyyar kara farashin wutan lantarki, Minista Saleh Mamman Credit: @EngrSMamman
Asali: Facebook

DUBA NAN: Shirin Dadin Kowa a Ramadan: Iyaye sun yi kira ga a canza lokacin shirin

A bangare guda, gwamnatin tarayya tayi watsi da rahoton bankin duniya wanda ya bayyana cewa kashi 78% na yan Najeriya na samun wutar lantarki ƙasa da awanni 12 a rana.

Gwamnatin ta bayyana haka ne a wani jawabi da mai baiwa shugaban ƙasa shawara ta musamman kan kayayyakin gwamnati, Mr. Ahmad Rufai Zakari, ya fitar a Abuja.

Mr. Zakari yace bankin bashi da ƙwakkwarar hujjar da yayi amfani da ita har ya gano wannan rahoton da ya fitar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel