Yan Najeriya na samun wutar Lantarki, Gwamnatin tarayya tayi watsi da rahoton bankin duniya

Yan Najeriya na samun wutar Lantarki, Gwamnatin tarayya tayi watsi da rahoton bankin duniya

- Gwamnatin tarayya tayi watsi da rahoton bankin duniya wanda ya nuna cewa mafi yawancin yan Najeriya na samun wutar lantarki ƙasa da awanni 12 a rana

- Mai baiwa shugaban ƙasa shawara ta musamman kan kayayyakin gwamnati, Mr. Ahmad Rufai Zakari, shine ya bayyana haka yayin da yake martani kan rahoton

- A cewarsa yan Najeriya na samun wutar lantarki dai-dai gwargwado kuma ana samun cigaba kullum

Gwamnatin tarayya tayi watsi da rahoton bankin duniya wanda ya bayyana cewa kashi 78% na yan Najeriya na samun wutar lantarki ƙasa da awanni 12 a rana.

Gwamnatin ta bayyana haka ne a wani jawabi da mai baiwa shugaban ƙasa shawara ta musamman kan kayayyakin gwamnati, Mr. Ahmad Rufai Zakari, ya fitar a Abuja.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari ne Babban Maƙiyin Haɗin kan Najeriya, inji shugaban ƙungiyar Yarbawa

Mr. Zakari yace bankin bashi da ƙwakkwarar hujjar da yayi amfani da ita har ya gano wannan rahoton da ya fitar.

Ya kuma jaddada cewa yan Najeriya na samun wutar lantarki dai-dai gwargwado, kuma ana samun cigaba kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Zakari, yayin da yake martani kan rahoton da bankin duniya ya fitar ranar Jumu'a, yace bai kamata bankin ya fitar da wannan rahoton ba, wanda bashi da tushe cewa kashi 78% na yan Najeriya na samun wuta ƙasa da awanni 12 a rana.

Yan Najeriya na samun wutar Lantarki, Gwamnatin tarayya tayi watsi da rahoton bankin duniya
Yan Najeriya na samun wutar Lantarki, Gwamnatin tarayya tayi watsi da rahoton bankin duniya Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

A jawabinsa yace:

"Ba dai-dai bane a fidda rahoto babu hujja cewa kashi 78% na yan Najeriya na samun wuta ƙasa da awanni 12 a rana. "

"A bayanan hukumar dake kula da wutar lantarki ta NERC, kashi 55% na yan Najeriya na cikin tsarin D da kuma E, waɗanda ke samar da wuta ƙasa da awanni 12 a rana."

KARANTA ANAN: Sanata Ali Ndume ya faɗawa gwamnatin tarayya matakin da yakamata ta ɗauka kan masu ɗaukar Nauyin Boko Haram

Hakanan kuma, Zakari ya sake yin watsi da rahoton bankin duniya da ya nuna cewa kashi 55% na yan Najeriya masu amfani da wutar lantarki basu da mitar gwajin wuta. Yace wannan rahoton bashi da tushe.

Yace: "Bamusan waye ya gudanar da wannan binciken ba kuma a wane lokaci a kayi binciken. Yan Najeriyan da suka samu kyautar mitar wuta, mun samu rahoton suna jin dadin amfani da ita."

Daga ƙarshe Zakari ya bayyana cewa ofishinsa na jin daɗin kyakkyawar alaƙar aikin dake tsakaninsa da bankin duniya. Saboda haka yayi mamakin da bankin ya fitar da wannan rahoton ba tare da tuntuɓar masu ruwa da tsaki a kan lamarin ba.

A wani labarin kuma Tsohon Sufetan Yan Sanda Ya Bayyana Hanyar da Gwamnati Zata Bi Ta Magance Matsalar Tsaro

Wani tsohon sufetan yan sandan ƙasar nan ya baiwa gwamnatin tarayya shawarar yadda zata yi ta daƙile matsalar tsaron ƙasar nan da jami'an yan sanda kawai.

Ya ce babu isassun yan sanda a ƙasar nan idan ka kwatanta da yawan jama'ar da Najeriya ke dasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel