Yan Boko Haram sun sake komawa Geidam, sun katse layukan kamfanonin sadarwan MTN da Airtel

Yan Boko Haram sun sake komawa Geidam, sun katse layukan kamfanonin sadarwan MTN da Airtel

- Kwana biyu a jere, yan Boko Haram sun kai hari jihar Yobe

- Karo na biyu yan ta'addan sun rabawa mutane wasiku

- Hakazalika sun kai hari na'urorin kamfanonin sadarwan MTN da Airtel

Mazaunan garin Geidam a jihar Yobe sun waye gari babu daman kira mutane da wayoyinsu sakamakon katse wayoyin kamfanonin sadarwan MTN da Airtel da yan ta'addan suka yi

Garin Geidam ne mahaifar mukaddashin Sifeto Janar na yan sanda, Usman Alkali, da kuma tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Geidam.

Da farko yan ta'addan sun kai hari garin da yammacin Juma'a, amma suka arce sakamakon ruwan wutan da Sojojin sukayi musu.

Ali Maina, daya daga cikin mazaunan garin ya ce bayan da Sojojin suka wuce, yan ta'addan suka dawo, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce: "Sun aikata ta'asa a garin da safen nan. Muna ganin gidan na konewa kuma sun fasa shaguna suna kwashe kayen abinci."

"Abin ya fi bamu tsoro yanzu, saboda bamu san manufarsu ba. An yankemu daga layukan MTN da Airtel saboda sun yanke abin."

"Yanzu muna neman kariyan Allah ne, suna da motocin Hilux sama da 15."

Bayan haka, kakakin hukumar yan sandan jihar Yone, Dungus AnduAbdulKarim ya tabbatar da sabon harin.

KU DUBA: Sai kun kara mana kudi zamu iya kawar da yan ta'adda, Shugaban Hafsan Soji Attahiru

Yan Boko Haram sun sake komawa Geidam, sun kona wayoyin kamfanonin sadarwa
Yan Boko Haram sun sake komawa Geidam, sun kona wayoyin kamfanonin sadarwa
Asali: UGC

KU KARANTA: Munanan hare-hare, garkuwa da mutane, da kashe-kashe 6 da suka auku jiya Laraba

A wani labarin daban, adadin mutanen da aka hallaka a jihar Zamfara na kara yawa yayinda rahotanni suka nuna cewa kawo yanzu akalla mutum 90 aka birne yayinda ake neman wasu da yawa.

Wadanda wannan mumunan hari ya shafa suka bada bayanin halin da ake ciki.

Gwamnatin jihar har yanzu bata bayyana adadin wadanda harin ya shafa ba yayinda take kira ga jami'an tsaro su tabbatar da tsaro a kauyuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel