Harin yan bindiga a Zamfara: An bizne mutum 90, har yanzu ana neman mutane da yawa

Harin yan bindiga a Zamfara: An bizne mutum 90, har yanzu ana neman mutane da yawa

- Har yanzu ana neman wadanda yan bindiga suka kashe a jihar Zamfara ranar Laraba

- Da farko an samu gawawwakin mutum 45 da aka kashe a karamar hukumar Gusau

- Sabbin rahotanni na nuna cewa har yanzu akwai mutane da dama da aka nema aka rasa

Adadin mutanen da aka hallaka a jihar Zamfara na kara yawa yayinda rahotanni suka nuna cewa kawo yanzu akalla mutum 90 aka birne yayinda ake neman wasu da yawa.

Wadanda wannan mumunan hari ya shafa suka bada bayanin halin da ake ciki.

Gwamnatin jihar har yanzu bata bayyana adadin wadanda harin ya shafa ba yayinda take kira ga jami'an tsaro su tabbatar da tsaro a kauyuka.

Mazauna Magami sun ce sun birne mutum 60 da safiyar Juma'a, bayan gano wasu gawawwaki 53.

Babban limamin kauyen, Sanusi Na'ibi, ne ya jagoranci Sallar Jana'izan.

An kawo gawwawaki ne daga sauran kauyuka dake kusa da Magami yayinda wasu basu samu daman kawo gawawwakin kauyensu cikin gari ba sun gudanar d nasu jana'izar.

"Karamar hukumar Gusau wannan mumunan hari yayi wa illa saboda yan bindigan kisa kawai suka zo yi ba sata ba," watan majiya ta bayyana.

KU KARANTA: Sai kun kara mana kudi zamu iya kawar da yan ta'adda, Shugaban Hafsan Soji Attahiru

Harin yan bindiga a Zamfara: An bizne mutum 90, har yanzu ana neman mutane da yawa
Harin yan bindiga a Zamfara: An bizne mutum 90, har yanzu ana neman mutane da yawa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Munanan hare-hare, garkuwa da mutane, da kashe-kashe 6 da suka auku jiya Laraba

Kun ji cewa wasu mutane da ake zargin 'yan fashi da makami ne sun jefa jihar Zamfara cikin jimami da juyayi bayan da suka kaddamar da hare-hare a garuruwa shida a ranar Laraba, 21 ga Afrilu, inda suka kashe akalla mutane 45.

A cewar jaridar Daily Trust, mutane da dama da suka hada da mata da yara sun bata a sanadiyyar hare-haren.

Legit.ng ta tattaro cewa yan fashin sun kuma lalata shaguna da gine-ginen gwamnati da masu zaman kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel