Dan Najeriya mai mata 7 ya bayyana dalar doyarsa a bidiyo mai bada mamaki

Dan Najeriya mai mata 7 ya bayyana dalar doyarsa a bidiyo mai bada mamaki

  • Wani dan Najeriya ya janyo maganganu a kafar sada zumunta bayan ya wallafa hoton gagarumar ma'adanar doyarsa
  • Mutumin mai suna Chief Goddey Ehiwarior yace ya kwashe sama da shekaru 40 yana hada wannan ma'adanar
  • A wani bidiyo da ya bazu, an ga ma'adanar doyan mai tsabar girma ta zarce ganin idon jama'a kuma ta burge matuka

Wani bidiyon magidanci dan Najeriya da ya wallafa ma'adanar doyarsa ta janyo maganganu kala-kala.

Babban manomin mai suna Chief Goddey Ehiwarior, ya wallafa bidiyon a Instagram wanda ya kunshi gagarumin ma'adanar doyarsa.

Goddey mai mata bakwai da 'ya'ya masu tarin yawa yace ya kasance yana noman doya sama da shekaru 45 da suka gabata.

Dan Najeriya mai mata 7 ya bayyana dalar doyarsa a bidiyo mai bada mamaki
Dan Najeriya mai mata 7 ya bayyana dalar doyarsa a bidiyo mai bada mamaki. Hoto daga @gossipboyz1
Asali: Instagram

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

"Ita Ta Nemeni Da Soyayya": Dan Jarida Makaho Yayi Tsokaci Kan Aure da rayuwarsa

Dan asalin jihar Deltan daga Amahia, Alihagwu da Agbor, tare da taimakon iyalinsa da ma'aikatansa ya mallaki ma'adanar doya mai girman gaske.

Goodey yace yana noman sauran kayayyakin bukata da suka hada da kubewa, tattasai, rogo da kwakwar man ja.

Mutumin mai tarin mata yace yana kiwon dabbobi. Bidiyon ya janyo maganganu daga jama'a inda wasu ke jinjina yadda ya kudance da abinci.

@validtilldate cewa tayi: "Idan kuwa wannan ne yake samu duk shekara, bai kai daya bisa hudun gonar doyan mahaifina ba. Wannan kadan ne idan aka hada su da ta mahaifina. Hakazalika doyan basu da girma sosai."

@foodbytener yace: "Abun alfahari, Allah yasa aikinmu tukuru ya biya mu wata rana."

@_mazi_brian_holmes ya rubuta: "Duba abinda kokariin shekaru 45 ya kawowa mutum daya. Ka kwatanta idan Najeriya tayi amfani da damarta a cikin shekaru 61. Abun takaici."

A wani labari na daban, mutuwar wani dan Najeriya kasa da sa'o'i biyu kafin bikin auren shi ya gigita jama'ar yankin Ikyangedu dake jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Yadda Budurwa Ta Kashe Saurayinta Da Wuka Cikin Dare Kusa Da Dakin Hotel

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, mota ce ta bige angon mai suna John Abugu yayin da yaje karbo rigar da zai saka wurin daurin auren daga shagon mai wanki da guga.

Amarya mai suna Rosemary Hudu, 'yar kasuwa ce wacce ta fada tsananin jimami bayan jin labarin mutuwar ango Abugu. A yayin bayyana damuwarta, Rosemary tace ta so a ce mutuwa tayi tare da angonata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel