Kada ka sauka daga Muƙaminka domin kowa nada nashi guntun kashin a baya, MURIC ga Sheikh Pantami

Kada ka sauka daga Muƙaminka domin kowa nada nashi guntun kashin a baya, MURIC ga Sheikh Pantami

- Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmai (MURIC),ta roki ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani da kar ya kuskura ya aje muƙaminsa

- A kwanan nan dai, Minista Pantami na shan suka kan wasu kalamai da yayi a baya dake nuna goyon baya ga wasu kungiyoyi amma daga baya ya ce ya canza matsaya akan waɗannan jawabai nasa

- Shugaban MURIC, frofessa Ishaq Akintola, ya ce mutum irin Pantami da ya bayarda rayuwarsa don cigaban Najeriya, goyon baya yakamata a bashi ba zargi ba

Ƙungiyar kare haƙƙin musumai (MURIC) ta roƙi ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Isa Pantami da ya watsar da kiran da wasu ke masa ya aje muƙaminsa.

KARANTA ANAN: PDP ta hurowa Shugaba Buhari Wuta, Ta nemi ya sallami Sheikh Pantami

Ana cigaba da kira ga ministan da ya sauka daga muƙaminsa saboda zargin da ake masa da hannu a ta'addanci, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Pantami ya bayyana kiran da ake masa ya ajiye muƙaminsa da siyasa, ya kuma canza maganganun da yayi a baya.

Amma duk da haka waɗanda ke kira ga shugaba Buhari ya sallamesa basu daina ba, sun cigaba da kiraye-kirayensu.

A wani jawabi da shugaban MURIC, Ishaq Akintola, ya fitar, yace:

"Wani sashin yaɗa labarai a Najeriya ya buga rahoton dake bayyana kiran da mutane keyi na Dr. Isa Pantami ya sauka daga muƙaminsa saboda labarin ƙarya dake cewa Amurka ta saka sunansa a cikin jerin sunayen yan ta'addan da suke nema."

"Da kuma zargi na biyu da ake ma ministan na wasu kalamai da yayi a baya. Wannan kiraye-kirayen basu da amfani kuma kamata yayi a watsar dasu."

"Pantami ya shiga Amurka a lokuta da dama a baya, har Facebook, dadandalin sada zumunta dake a Amurka, sun saka hoton Pantami a hukumance na tsawon awanni domin giramama shi a wata ziyara daya kai ƙasar."

Kada ka sauka daga Muƙaminka domin kowa nada tasa badaƙalar a baya, MURIC ga Sheikh Pantami
Kada ka sauka daga Muƙaminka domin kowa nada tasa badaƙalar a baya, MURIC ga Sheikh Pantami Hoto: dailypost.ng
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Ministan Sadarwa Isa Pantami ya nesanta kansa da wasu kalmomi da yayi a baya kan Wasu ƙungiyoyin Yan ta'adda

Shugaban MURIC ɗin yace, duk wannan abun shiryayye ne saboda a yaƙi tsarin da gwamnatin tarayya ta fito dashi na haɗa NIN da layin waya.

"Babu wani ɗan Najeriya wanda yake ƙaunar ƙasar mu Najeriya da zai goyi bayan wannan zarge-zargen da ake ma babban mutum mai mutunci kamar Pantami" Akintola ya faɗa.

Ƴace Kowa ya san cewa tsarin haɗa NIN da layin waya tsari ne da zai tona asirin yan ta'adda kamar yan fashin asusu, yan bindiga, yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane da suke amfani da intanet ko wayar salula wajen gudanar da aikinsu.

Ishaq Akintola ya ƙara da cewa mutumin da ya bada rayuwarsa wajen ƙoƙarin gyara Najeriya kamata yayi a nuna masa goyon baya.

A wani labarin kuma Yan sanda sun kama wata mata da zargin ta kashe ɗan kishiyarta da guba

Rundunar yan sandan jihar Enugu ta kama wata matashiyar mata da zargin kisan ɗan kishiyarta.

Matar da ake zargin ta amsa laifinta, amma tace ta yi haka saboda mijinta baya bata kulawa sam da ita da yayanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel