PDP ta hurowa Shugaba Buhari Wuta, Ta nemi ya sallami Sheikh Pantami
- Babbar jam'iyyar adawa PDP ta hurawa shugaba Buhari wuta kan ya sallami ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Isa Pantami
- Shugaban jam'iyyar na ƙasa, Uche Secondus, shi ne ya yi kira ga shugaban da ya sallami ministan matuƙar bai aje muƙaminsa da kansa ba
- Ya ce yan Najeriya da kuma tsaron ƙasa basa bukatar Pantami a cikin ofis a yanzun, kamata yayi ya aje aikinsa ya kuma baiwa yan Najeriya hakuri
Babbar jam'iyyar hamayya PDP tace babu dalilin da zaisa shugaba Buhari ya cigaba da zama da Ministan Sadarwa da tattalim arzikin zamani, Isa Pantami, a mstsayin ɗaya daga cikin mamban majalisar zartarwa.
KARANTA ANAN: Ministan Sadarwa Isa Pantami ya nesanta kansa da wasu kalmomi da yayi a baya kan Wasu ƙungiyoyin Yan ta'adda
Yanzu haka dai an hurowa ministan sadarwa wuta kan wasu kalamai da ya yi a baya da suka nuna goyon baya ga ƙungiyar Alƙa'ida da Taliban.
Jam'iyyar PDP tace saboda waɗannan raɗe-raɗin dake yawo akansa, babban abinda ya kamata shine ya ajiye muƙaminsa.
Bayan ya ajiye muƙamin nasa kuma ya roƙi yan Najeriya gafara a kan wuce gona da iri da ya yi a a baya.
Shugaban jam'iyyar ta PDP, Uche Secondus, wanda ya yi wannan jawabi ga wakilin Punch, ya kira yi shugaba Buhari da ya sallameshi idan yaƙi ya ajiye muƙaminsa dan karan kansa.
KARANTA ANAN: Yan sanda sun kama wata mata da zargin ta kashe ɗan kishiyarta da guba
A bayaninsa, Uche Secondus, ya ce:
"Babban abinda yafi kamata ministan yayi a yanzun shine ya sauka daga matsayinsa, kuma ya fara wa'azi kan hatsarin ta'addanci a fili kowa yasan yana yi."
"Amma a yanzun yan Najeriya da kuma tsaron ƙasa basa bukatar cigaba da kasan cewarsa a ofis din minista."
Uche yace ya kamata ace masu riƙe da muƙamai su koyi ɗabi'ar ajiye aiki idan ana zargin su da aikata wani abu ba dai-dai ba.
A wani labarin kuma Kotu ta yanke ma fitacciyar jarumar shirya fina-finai hukuncin watanni uku a gidan yari saboda hoton tsiraici
An yanke ma jarumar hukuncin ne bayan ta aikata laifin bayyana hoton tsiraici a shafinta na kafar sada zumunta.
Jarumar wacce aka fi sani da Akuapem Poloo, ta amsa laifinta bayan ta bayyana a gaban kotu.
Asali: Legit.ng