Da duminsa: Bayan sa'o'in kadan da zuwan ministan tsaro, Boko Haram sun kai farmaki Borno

Da duminsa: Bayan sa'o'in kadan da zuwan ministan tsaro, Boko Haram sun kai farmaki Borno

- Mayakan ta'addanci na Boko Haram sun kai farmaki garin Dikwa dake jihar Borno

- Wannan harin yana zuwa ne bayan sa'o'i kadan da ministan tsaro da hafsoshin tsaro suka je Maiduguri

- 'Yan ta'addan sun yi musayar wuta da sojoji wurin karfe 7 na yammacin Lahadi inda suke son kustawa garin Dikwa

Kasa da sa'o'i hudu bayan ziyarar da minsitan tsaro, Bashir Magashi tare da hafsoshin tsaro zuwa Maiduguri, mayakan Boko Haram sun kai farmaki karamar hukumar Dikwa dake jihar Borno a ranar Lahadi.

Dikwa tana yankin tsakiyar jihar Borno ne kuma tana da nisan kilomita 85 zuwa babban birnin jihar na Maiduguri, Vanguard ta ruwaito.

Bayanan da aka samu daga majiyoyi sun tabbatar da cewa, mayakan ta'addancin dauke da makamai da motocin yaki a halin yanzu suna musayar wuta da jami'an tsaro domin su samu kutsawa garin.

Suna son shiga domin tada zaune tsaye. Karar harbe-harbe ta fashe-fashe ya gwauraye yankin wurin karfe 7 na ranar Lahadi.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindigan da suka sace daliban Kaduna suna bukatar N500m

Da duminsa: Bayan sa'o'in kadan da zuwan ministan tsaro, Boko Haram sun kai farmaki Borno
Da duminsa: Bayan sa'o'in kadan da zuwan ministan tsaro, Boko Haram sun kai farmaki Borno. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: UGC

KU KARANTA: Ban sake bacci ba tun bayan da aka kashe sojoji a Benue, Ortom

Dikwa tana fuskantar jerin miyagun hare-hare daga mayakan ta'addanci a cikin kwanakin nan.

Daruruwan mayakan ISWAP ne suka tsinkayi sansanin sojoji na garin Dikwa. Majiyoyi masu karfi sun sanar da cewa mayakan ISWAP da sojojin sun dinga musayar wuta har wurin karfe 10 na daren Lahadi.

Daya daga cikin majiyoyin sun ce 'yan ta'addan sun hari Dikwa ta bangarori daban-daban amma zakakuran sojoji ne suka hana su shiga.

"Maharan suna bukatar kayan yaki ne kuma hakan yasa suke ta kai hari sansanin sojoji. Ba fatansu su kwace gari ba, makamai suka bukata.

"Suna kai hari kauyuka ne domin samun kayan abinci amma kamar yadda kuma ake gani idan sun yi nasara tafiyarsu suke yi," majiya tace.

A wani labari na daban, hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta cafke wasu 'yan kasar Chadi da Nijar dake samarwa miyagun 'yan ta'adda kwayoyi a Najeriya.

An cafkesu ne a makon da ya gabata a jihohin Taraba da kuma Nijar, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa, ya bayyana hakan a Abuja yayin da shi tare da kungiyarsa suka ziyarci ministan yada labarai da al'adu na kasar nan, Lai Mohammed.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel