Mutanen Arewa fiye da 100 sun tsere daga Imo bayan an hallaka ‘Yanuwansu 'haka-kurum'

Mutanen Arewa fiye da 100 sun tsere daga Imo bayan an hallaka ‘Yanuwansu 'haka-kurum'

- Wasu mutanen jihohin Arewa su na barin Imo saboda matsalar rashin tsaro

- Rahotanni sun tabbatar da cewa fiye da mutum 100 sun koma garuruwansu

- Gwamnan jihar Imo ya roki wadanda su ka fito daga Arewan su yi zamansu

‘Yan bindiga sun kashe karin mutanen Arewa takwas, yayin da aka ji wa wasu shida rauni a danyen hare-haren da su ka kai a jihar Imo a makon jiya.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa wannan hare-hare sun sa ‘Yan Arewa sun shiga cikin halin dar-dar da zaman firgici a jihar Kudu maso gabashin kasar.

A dalilin wannan mummunan lamari da ya ke auku wa, wasu mutanen da su ka fito daga Arewa sun fara kaura daga Imo, da-dama daga cikinsu sun koma gida.

KU KARANTA: Imo: Wasu 'yan bindiga sun banka a wuta ofishin 'yan sanda

Wani ‘dan kasuwa a Imo, Iliyasu Sulaiman, ya shaida wa ‘yan jarida cewa an harbe ‘danuwansa na jini, sannan an kashe wasu mutanen Arewa uku a garin Orlu.

“Mun birne mutane takwas, sannan wasu mutane shida su na jinya a asibiti.” Inji Alhaji Iliyasu Sulaiman.

‘Dan kasuwan ya koka da cewa: “Ba mu san musababbin wannan abu ba, domin ba mu tsokano fada da kowa ba, amma su na ta kashe mutanenmu kamar hauka.”

A cewarsa, wannan kashe-kashe da ake yi ya tilasta wa fiye da mutane 100 sun bar Imo, sun koma inda su ka fito a cikin makonni biyun nan da su ka wuce.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kubutar da fursunoni sama da 2,000 a Kudu

Mutanen Arewa fiye da 100 sun tsere daga Imo bayan an hallaka ‘Yanuwansu 'haka-kurum'
Gwamnan Imo, Sen. Hope Uzodinma
Asali: Facebook

“Kawo yanzu na san mutane kusan 60 da su ka koma Sokoto, wasu fiye da 20 sun koma Kano da Katsina, sannan wasu su na shirin yin kaura.” Inji ‘dan kasuwar.

Alhaji Sani Ahmad Mai Rago ya ce baza jami’an tsaro a yankin Hausawa a Owerri kadai bai isa ba domin 30% na ‘Yan Arewa ne kadai su ke cikin aminci a yanzu.

Gwamnatin jihar Imo ta sha alwashin kare mutanen Arewan tare da lallashinsu su zauna a garin. Wani hadimin gwamnan ya musanya cewa wasu su na barin gari.

A makon da ya gabata ne ku ka samu labarin wasu 'Ƴan bindiga sun kai hari ofishin ƴan sanda a jihar Imo, inda su ka sace wani jami'i, sannan su ka raunata wasu.

Bayan an yi wata fafatawa da jami'an tsaro, 'yan bindigan sun yi nasarar sace wani 'dan sanda, kuma su ka fito da duk wadanda jami'an tsaron su ke tsare da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng