Mutum 40 kacal suka halarta bana sabanin 300 a bara: Mai shirya liyafar murnar dawowar Buhari

Mutum 40 kacal suka halarta bana sabanin 300 a bara: Mai shirya liyafar murnar dawowar Buhari

- Bayan makonni biyu a Landan, Buhari ya dawo Najeriya

- Wani dan a mutum Buhari ya shirya walima na musamman don murnar haka

- Wannan shine karo na takwas da zai shirya irin wannan liyafa

Mai shirya liyafar murnar dawowar Buhari duk lokacin da yaje jinya ya ce mutum 40 suka halarta bana sabanin 300 a bara.

Wani dan a mutun Buhari, Abubakar Rabiu, ya shirya taron walima ta musamman don murnar dawowar shugaba kasan daga birnin Landan inda yaje hutawa ko jinya.

Da yammacin Juma'a yayin rana ta fadi kuma lokacin shan ruwa yayi, Abubakar Rabiu, ya tara jama'a a wani gidan cin abinci dake gaban jami'ar tarayya a Dutsinma, jihar Katsina.

Rabiu, wanda aka fi sani da Abu albarka, ya kasance babban masoyin shugaba Buhari kuma ya kasance yana yanka rago don walima duk lokacin da Buhari yayi tafiya ya dawo - musamman na jinya.

A cewar Daily Trust, wannan shine karo na takwas da zai shirya liyafa.

DUBA NAN: An hallaka yan kasuwan Arewa a sabon harin da aka kai jihar Imo

Mutum 40 kacal suka halarta bana sabanin 300 a bara: Mai shirya liyafar murnar dawowar Buhari
Credit: @daily_trust
Mutum 40 kacal suka halarta bana sabanin 300 a bara: Mai shirya liyafar murnar dawowar Buhari
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jerin jihohi 5 da suka fi aiwatarwa al'ummarsu manyan ayyuka na kasafin kudi, Kaduna ce ta farko

Abokansa masoya Buhari sun samu halartan wannan liyafa inda suka yi addu'an Allah ya karawa shugaban kasa lafiya.

"Bana mutum 40 suka halarta don shan ruwa. Wannan shine adadi mafi karancin da muka samu, la'lla saboda azumin Ramadanda ne, bara kimanin mutum 300 suka halarta," yace.

Abu Albarka ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari nan matukar kokari wajen magance matsalar tsaro da karfafa tattalin arziki.

Ya yi kira ga yan Najeriya su cika da addu'a ga shugabannin Najeriya don zaman lafiya da cigaba.

Mun kawo labarin cewa shugaba Muhammadu Buhari ya dira babban tashar jirgin kasa da kasa ta Nnamdi Azikwe dake birnin tarayya Abuja daga birnin Landan bayan makonni biyu inda yaje ganin Likita.

Buhari ya dira Abuja ne misalin karfe 5 na yammacin Alhamis, 15 ga Afrilu 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel