Yanzu yanzu: Yan bindiga sun hallaka mutum 6, sun jikkata 3 a Jihar Plateau

Yanzu yanzu: Yan bindiga sun hallaka mutum 6, sun jikkata 3 a Jihar Plateau

-Yan bindiga sun hallaka mutane shida a karamar hukumar Riyom dake jihar Filato

_Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar ne ya bayyanawa manema labarai

-Sai da yan bindigan suka sanar da mutanen kauyen kafin su kai harin

Akalla mutane 6 sun rasa rayuwar, 3 sun jikkata yayinda yan bindiga suka kai hari kauyen Wereng a karamar hukumar Riyom na jihar Plateau a daren Alhamis, Jaridar Daily trust ta ruwaito

Idan zaku tuna waccan satin mutane takwas sun rasa rayuwarsu a kauyen Kuru a karamar hukumar.

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Riyom, Timothy Dantong ne ya bayyanawa manema labarai ranar Juma'a.

KU KARANTA: Wadanda suka yi garkuwa da dalibai a Kaduna sun fara kiran iyayen domin kudin fansa

Yanzu yanzu: Yan bindiga sun hallaka mutum 6 sun jikkata 3 a Jihar Plateau
Yanzu yanzu: Yan bindiga sun hallaka mutum 6 sun jikkata 3 a Jihar Plateau Source: Twitter
Asali: Twitter

KU KARANTA: NDLEA ta damke 'yan kasar Chadi da Nijar dake samarwa 'yan ta'adda miyagun kwayoyi

Yace sunji cewar zaa kawo hari kauyen amma mutanen garin suka cigaba da harkokinsu saboda basu aikata wani laifi ba.

Ya kara da cewa "Kawai na tashi da safiyar yau juma'a ne naji labarin yan bindiga sun kashe shida daga cikin mutane na yayinda suka kawo hari kauyen Wereng a darn jiya(Alhamis)."

A makon jiya, mun kawo muku cewa Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa Najeriya na cikin halin rashin kudi saboda sai da aka buga wasu biliyoyi a watan Maris aka rabawa jihohi.

Amma a ranar Laraba Gwamnatin tarayya ta siffanta kalaman gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, na cewa an buga kudi N60bn don rabawa gwamnoni a matsayin karya maras tushe da asali.

Ministar kudi da kasafi, Zainab Ahmed Shamsuna, ta bayyana hakan yayin hira da manema labaran fadar shugaban kasa ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel