Wadanda suka yi garkuwa da dalibai a Kaduna sun fara kiran iyayen domin kudin fansa

Wadanda suka yi garkuwa da dalibai a Kaduna sun fara kiran iyayen domin kudin fansa

-Wadanda suka yi garkuwa da dalibai a Kaduna sun fara neman iyaye domin amsar kudin fansa

-Sun bayyana cewa zasu kashe daliban idan ba'a biya musu bukatunsu ba

-Sheikh gumi ya bayyana dalilin da yasa masu garkuwar suka ki sakin daliban

Rahoton daga Daily Nigerian na nuna cewa yan bidigan da suka yi garkuwa da dalibai a Kaduna sun fara tuntubar iyayensu domin amsar kudin fansa.

Wakilan jaridar sun tattaro daga iyayen yaran cewa yan bidigan sun fara kiransu a waya sunce zasu kashe yaran idan ba'a cika bukatunsu ba.

Daya daga cikin iyayen daliban ya bayyanawa yan jarida cewa : "Sun umurci diyata da ta kirani a waya tana kuka tana rokona da na basu kudin fansar idan ba haka ba zasu kashe ta."

Wata mahaifiyar daya daga cikin yaran ta bayyana cewa yan bindigan sun ce mata idan basu biya N500m ba to bazasu sake ganin diyarsu ba.

KU KARANTA: Ba ni na raba shinkafa a Kano ba amma ina godiya ga wadanda sukayi, Tinubu

Wadanda suka yi garkuwa da dalibai a Kaduna sun fara kiran iyayen domin kudin fansa
Wadanda suka yi garkuwa da dalibai a Kaduna sun fara kiran iyayen domin kudin fansa Hoto: @PraesidioLtd Source: Twitter
Asali: Twitter

kU KARANTA: Da gaske mun buga kudi, amma rance muka baiwa gwamnoni: Gwamnan CBN

Ahalin yanzu, Babban Malamin nan, Sheikh Gumi, ya bayyana abinda yasa masu garkuwar suka ki sakin daliban na makarantar raya gandun daji dake Kaduna.

Yayin zantawa da manema labarai ranar Alhamis, 25 ga watan Maris ya bayyana cewa akwai tsoro matuka a zukatan yan bindigan tun bayan da gwamnati ta bada umurnin harbe duk wanda aka kama da Ak47.

Yace yan bindigan suna ankare sosai da wanda ya matso kusa da su saboda suna tsoron ko tana iya yiwuwa yana aiki da gwamnati.

Shehin Malamin ya kara da cewa yan bindigan da ya gana dasu kwanan nan sun fada masa cewa sun san shugaban wanda yayi garkuwa da daliban, amma duk wani yunkuri na samunsa yaci tura tun bayan umarnin da gwamnati ta bayar.

Gumi yace: "A halin yanzu, Kwarewar mu ta kai da zaran munga wani dan ta'adda zamu gane shi. Mun gano shugaban wadanda suka yi garkuwa da daliban amma bai taba halartar wani taron sasanci da mu ba.

"Yan bidigan da muka hadu dasu sun bayyana mana shi amma bamu samu ganinshi ba saboda umarnin da gwamnati ta bada na harbe duk wanda aka gani da AK 47 da kuma cewa ba zata yi sasanci da yan bindiga ba. Saboda haka banaso mu shiga cikin daji domin kada gwamnati tayi tsammanin muna kara musu karfin gwiwa ne."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng