Babu kudi a Najeriya, sai da aka buga sabbin kudi N60bn aka raba mana a watan Maris, Gwamna Obaseki

Babu kudi a Najeriya, sai da aka buga sabbin kudi N60bn aka raba mana a watan Maris, Gwamna Obaseki

- Gwamna Obaseki na jihar Edo ya fasa kwai kan kudin da aka raba musu a Maris

- Obaseki ya ce mutane su daina ganin laifin Buhari, ba boka bane

- Obaseki ya ce tattalin arzikin Najeriya ya lalace kawai kame-kame akeyi

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa Najeriya na cikin halin rashin kudi saboda sai da aka buga wasu biliyoyi a watan Maris aka rabawa jihohi.

Gwamnan ya ce kudin wata-wata da ake rabawa gwamnoni bai kai ba, sai da gwamnatin tarayya ta buga sabbin kudi bilyan 50 zuwa 60 aka raba musu.

"Lokacin da aka biyamu kudin wata-wata na Maris, sai da gwamnatin tarayya ta buga N50-N60 billion don kudin su isa a raba mana," Obaseki ya bayyana ranar Alhamis.

"A wannan watan na Afrilu, zamu sake komawa Abuja a raba mana kudi. A karshen shekarar nan adadin bashin da muka ci zai zama tsakanin N15-N16 trillion."

"Kawai karban bashin kudi akeyi babu hanyar biya, amma hankalin kowa na kan 2023, kowa na ganin laifin shugaban kasa sai kace boka ne."

"Najeriya ta canza. Tattalin arzikin Najeriya ya canza gaba daya tun bayan yakin basasa, kawai kame-kame mukeyi."

KU KARANTA: Rikici ya barke wajen zaben shugabannin PDP a Kaduna

Babu kudi a Najeriya, sai da aka buga sabbin kudi N60bn aka raba mana a watan Maris, Gwamna Obaseki
Babu kudi a Najeriya, sai da aka buga sabbin kudi N60bn aka raba mana a watan Maris, Gwamna Obaseki Credit: Presidency

KU KARANTA: Mun yarda sojoji mata su sanya Hijabi idan zai karesu daga harsashi: Kungiyar CAN

A wani labarin kuwa, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi bayanin yadda uwargidarsa, Hajiya Aisha Buhari, ta taimakawa rayuwar yan Najeriya ta hanyoyi daban-daban.

A jawabin gabatarwa da yayi a sabon littafinta da aka kaddamar ranar Alhamis kuma bai samu halarta ba, Buhari ya ce wannan littafin ya bashi daman fadin wasu kalamai akan uwargidarsa.

Ya ce Aisha, karkashin shirinta na 'Future Assured' ta na cika burinta na taimakawa talakawa, marasa lafiya da marasa galihu har a karkara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel