Kwashe kimanin bilyan 8 a sirrance: Majalisa ta sammaci Ministar Kudi da AGF

Kwashe kimanin bilyan 8 a sirrance: Majalisa ta sammaci Ministar Kudi da AGF

- Shugaban hukumar NADDC, Jelani Aliyu, ya shigar da karan wasu ministocin Buhari gaban majalisa

- Duk da cewa ba su suka aikata zargin da ake musu ba, majalisa ta sammacesu

- Ministar Kudi da gwamnan Edo suna tuhumar juna da karya kan maganar buga kudi N60bn

Majalisar dattawa ta sammaci Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmad, da Akawunta Janar na kasa, Ahmed Idris, kan kwashe kudi N7.5bn daga asusun ma'aikatar inganta kera motoci NADDC a boye.

Kudin ma'aikatar kwamanin bilyan takwas na ajiye ne a babbar bankin kasa CBN.

An cire N3.8bn a shekarar 2000 sannan aka cire N3.8bn; N2.8bn a 2005 da N1bn a 2006, a cewar rahoton daga ofishin Odita Janar na kasa.

Kwamitin majalisar kan kudin al'ummar karkashin Sanata Matthew Urhoghide na shirin kaddamar da bincike kan rahoton.

Dirakta Janar na ma'aikatar NADDC, Jelani Aliyu, ya bayyanawa yan majalisan cewa an cire wadannan kudade ba tare da sanin ma'aikatarsa ba.

Ya ce hukumar ta dade tana kokarin amsan kudinta amma abin ya ci tura.

Saboda haka, kwamitin ta aika sakon sammaci ga gwamnatin tarayya ranar Laraba.

KU KARANTA: Pantami ya cire takunkumin rijistan layin waya, yace a cigaba da gashi

Kwashe kimanin bilyan 8 a sirrance: Majalisa ta sammaci Ministar Kudi da AGF
Kwashe kimanin bilyan 8 a sirrance: Majalisa ta sammaci Ministar Kudi da AGF Credit: (Photo: @ZShamsuna, @nilsnigeria)
Asali: Twitter

DUBA NAN: Shugaba Buhari ya dawo Najeriya bayan hutawa a Landan

A bangare guda, Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya bayyana cewa ba zai yi cacan baki da gwamnatin tarayya kan maganar da yayi na cewa an buga N60bn a Maris don rabawa gwamnoni.

A ranar Laraba Ministar kudi da kasafi, Zainab Ahmed Shamsuna, ta siffanta kalaman gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, na cewa an buga kudi N60bn don rabawa gwamnoni a matsayin karya marasa tushe da asali.

Obaseki yace; "Maimakon kame-kame, muna kira ga gwamnati ta dau mataki wajen kawo karshen almubazzaranci don dakile tabarbarewan tattalin arzikin kasar."

Asali: Legit.ng

Online view pixel