Wata Budurwa ta yi watsi da tayin aure saboda tsantsangaron kaunar Rabiu Kwankwaso

Wata Budurwa ta yi watsi da tayin aure saboda tsantsangaron kaunar Rabiu Kwankwaso

- Wata Budurwa ta fito ta bayyana yadda ta ke jarabar kaunan Rabiu Kwankwaso

- Wannan Baiwar Allah ta ce za ta iya mutuwa a dalilin son da ta ke yi wa Madugu

- Lubna Ali ta ce a wurin ta Sanata Kwankwason ya fi karfin a ce masa ‘Dan siyasa

Wata Baiwar Allah mai suna Lubna Ali ta jawo abin magana bayan ta bayyana irin tsananin soyayyar da ta ke yi wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Lubna Ali a shafinta na Twitter, ta bayyana cewa a dalilin kaunar da ta ke yi wa Madugun Kwankwasiyya, ta ki amsa tayin aure da wani ya yi mata.

Wannan budurwa ta yi magana da jaridar Sahelian Times inda ta sake tabbatar da cewa ba za ta taba auren duk saurayin da bai ganin mutuncin gwarzonta ba.

KU KARANTA:

A cewarta, ba ta ki ta zauna babu miji a rayuwa ba, in dai sai ta auri mara ganin darajar Kwankwaso.

Lulualee kamar yadda aka san ta a Twitter ta bayyana cewa ko da ita ba ta harkar siyasa, amma ta na matukar kaunar tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso.

“Na kashe batun neman aure na saboda Mai girma, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, ko da bai sanni ba. Zan iya mutu wa saboda shi (Kwankwaso).” Inji Lubna Ali.

Ta ce: “Kwankwaso ya fi karfin ‘dan siyasa, ina yi masa kallon jagora ne, uba, kuma abin koyi.”

Wata Budurwa ta yi watsi da tayin aure saboda tsantsangaron kaunar Rabiu Kwankwaso
Kwankwaso da Lubna Hoto: saheliantimes.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Ana so Musulmai su dage tsayin-daka wajen ibada a Ramadan - Daurawa

Wannan Baiwar Allah ta ce ta fara sha’awar tafiyar Kwankwasiyya ne tun 2003, a lokacin ta na aji daya a sakandare, ta ce a lokacin ba ta ma san kan siyasa ba.

“Amma sunan Sanata Kwankwaso ya yi ta yawo a kai na. Zan tuna motar farko da na yi, kirar 406 ce mai launin ja dauke da hoton Kwankwaso ko ina a jikinta.”

Dazu kun ji cewa uwar jam'iyyar PDP ta bayyana kokarin da ta ke yi a kan rigimar su Rabiu Kwankwaso, Aminu Wali, Aminu Tambuwal da sauransu.

Manyan PDP za su dinke barakar da aka samu tsakanin 'Yan Kwankwasiyya da Magoya bayan Tambuwal da ake zargin su na marawa Sanata Bello Gwarzo baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel