Rikicin cikin-gida: Jam’iyyar PDP za ta sasanta Sanata Kwankwaso da Tambuwal

Rikicin cikin-gida: Jam’iyyar PDP za ta sasanta Sanata Kwankwaso da Tambuwal

- Jam’iyyar PDP za ta sasanta Rabiu Kwankwaso da Gwamna Aminu Tambuwal

- PDP ta bayyana cewa akwai shirin da ta ke yi na kashe wutar cikin gidan na ta

- Kola Ologbondiyan ya ce za a samu lokaci a karasa zaben Arewa maso yamma

Daily Trust ta ce jam’iyyar PDP ta fara kokarin sasanta rigimar da ake yi a game da zaben shugabannin jam’iyya na reshen Arewa maso yamma.

Rahotanni sun bayyana cewa manyan jam’iyyar adawar kasar za su shiga tsakanin gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da Rabiu Musa Kwankwaso.

Haka zalika jam’iyyar za ta shawo kan sabanin da aka samu tsakanin tsohon gwamnan na jihar Kano da tsohon Ministan waje, Ambasada Aminu Wali.

KU KARANTA: Tsohon Gwamna Shekarau zai gina titi a Mahaifar Kwankwaso a Kano

An samu sabani a wajen zaben shugabannin PDP na shiyyar Arewa maso yamma inda magoya bayan Aminu Tambuwal su ka gwabza da ‘Yan Kwankwasiyya.

Rigima ta barke ne a jam’iyyar a dalilin kujerar mataimakin shugaban jam’iyya da aka ware wa jihar Kano, a karshe dai dole aka hakura aka dakatar da zaben.

A jihar Kano ana takun saka tsakanin ‘Yan Kwankwasiyya wanda turakun jam’iyyar hamayyar ta ke hannunsu da kuma magoya bayan Ambasada Aminu Wali.

Da aka shiga zaben shiyyar Arewa maso yamma, ‘Yan Kwankwasiyya sun tsaida wanda zai yi takara, sai dai sun gamu da adawa daga bangaren hamayyarsu.

Rikicin cikin-gida: Jam’iyyar PDP za ta sasanta Sanata Kwankwaso da Tambuwal
Gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal

KU KARANTA: “Kai kuma a wa?” – ‘Yan Jam’iyya sun juya wa Ministan N/Delta baya

Sakataren yada labarai na PP na kasa, Kola Ologbondiyan, ya tabbatar da cewa ana kokari ta karkashin kasa domin a sasanta jiga-jigan jam’iyyar da ke rigima.

“Kun san mu na watan Azumi ne yanzu, saboda haka ba mu sani ba. Amma mun nemi jagororin Arewa maso yamma su fito da lokacin da za a shirya zaben.”

Ologbondiyan ya ce: “Mun yi kira ga shugabannin Arewa maso yamma su fara shirin sulhu, yayin da uwar jam’iyya za ta yi na ta kokarin sasanta masu rikicin.”

A makon jiya kun ji ana rigima a jam'iyyar PDP ta reshen arewa maso yamma inda ake musayar yawu tsakanin Sanata Rabiu Kwankwaso da Aminu Tambuwal.

Kwankwaso ya zargi Tambuwal da katsalandan cikin harkokin jam’iyyar PDP a jihar Kano, ya ce gwamnan ya na goyon bayan wanda ya yi wa PDP zagon-kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel