Goron Ramadan: Abubuwa 10 da ya kamata kowane Musulmi ya kiyaye da Azumi - Daurawa

Goron Ramadan: Abubuwa 10 da ya kamata kowane Musulmi ya kiyaye da Azumi - Daurawa

A wata zanta wa da BBC Hausa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi magana game da abubuwan da ake bukatar mai azumi ya kiyaye su.

Kamar yadda babban malamin addinin Musuluncin ya bayyana, akwai bukatar wanda ke azumi a bakinsa ya kula da wadannan abubuwa har goma.

Hakan ya na zuwa ne a daidai lokacin da kusan duka musulman Duniya su ka dauki azumin watan Ramadan a yau Talata, 13 ga watan Afrilu, 2021.

Kamar yadda Aminu Ibrahim Daurawa ya yi bayani, ana so duk wanda ya dauki azumi a bakinsa ya dage wajen tsaida salloli na farilla da na nafila.

Har ila yau, malamin ya bayyana cewa ciyarwa ya na amfani ta yadda duk wanda ya dace da ciyar da mai azumi, zai samu ladar wannan mutum.

KU KARANTA: Duk wanda ya sabawa ganin watan Sarkin Musulmi ya bar Sunnah - PenAbdul

A lokacin azumi muslumai su na da damar yin addu’o’i a wasu lokuta na musamman da ake amsa addu’a.

1. Azumi: Ya kamata mutum ya inganta azuminsa, ya yi amfani da ilmi.

2. Sallah: Ana so duk mai azumi ya dage wajen tsaida sallolin farilla, nafilolin ‘rawatib’ da kuma sallar tarawih.

3. Ciyarwa: Ciyarwa ta na da muhimmanci a watan Ramadan, an so mutum ya bada sadakar ko da ruwa ne saboda dinbin ladar.

4. I’itikafi: Ana so a maida hankali wajen shiga I’itiqafi idan har mutum ya na da hali.

5. Lailatul-Qadr: Neman dare mai alfarma na Lailatul-Qadr ya na da matukar falala.

Goron Ramadan: Abubuwa 10 da ya kamata kowane Musulmi ya kiyaye da Azumi - Daurawa
Malam Aminu Daurawa
Asali: UGC

KU KARANTA: Fa'idojin watan Ramadan - Daga bakin Bn Othman

6. Afuwa: Ka da mutum ya kuskura ya rika azumi alhali ya na jin haushin wani.

7. Tilawa: Addini ya bukaci mutane su shagala da karatun Kur’ani a cikin wannan watan.

8. Addu’a: Ana amsa addu’o’i a lokacin sahur, bude baki da cikin tsakiyar azumi.

9. Zumunci: Sada zumunta a watan Ramadan ya na da amfani, ya na da kawo lada da arziki.

10. Tausayi: Ana so bayan Ramadan mutum ya zama ya koyi tausayin taimaka wa mabukata.

A wannan hirar, fitaccen malamin addinin ya ambaci falolin yin afuwa domin samun rahamar Ubangiji da kuma ladar da ake samu wajen sada zumunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel