Yanzu-yanzu: An ga wata a Najeriya, gobe za'a tashi da azumi: Kwamitin duban wata

Yanzu-yanzu: An ga wata a Najeriya, gobe za'a tashi da azumi: Kwamitin duban wata

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa an ga jinjirin watan Ramadana a wurare daban-daban a Najeriya, mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar.

Hakazalika Kwamitin neman wata a Najeriya ce tayi wannan sanarwa a shafinta na Tuwita.

A jawabin da yayi kai tsaye, Sarkin Musulmi ya ce an ga watan Ramadana na shekarar 1442 AH.

Ya yi kira ga Musulmai su fara azuni kuma su koma ga Allah lokacin wannan wata mai alfarma.

Ya bukacesu su roki Allah ya kawo karshen matsalar tsaro da annobar Korona a Najeriya.

Sultan ya yi addu'an cewa Allah ya baiwa Musulami daman gabatar da ibadunsu kuma ya yi kira ga Musulman su bi dokokin da aka gindaya na kariya daga annobar Korona.

A jawabin da majalisar koli ta sharia'ar Musulunci a Najeriya NSCIA ta saki, tace: "NSCIA karkashin jagorancin shugabanta kuma Sultan na Sokoto na sanar da daukacin al'ummar Musulmi cewa an ga jinjirin watan Ramadana a yau 12/04/2021 wanda yayi daidai da 29 Sha’aban. 1442AH.

"Saboda haka gobe, 13 ga Afrilu, 2021 ne 1 ga watan Ramadan 1442AH."

KU KARANTA: APC ta raba kayan Abinci cike da Manyan Motocin ɗaukar kaya 130 ga talakawa

Yanzu-yanzu: An ga wata a Najeriya, gobe za'a tashi da azumi: Kwamitin duban wata
Yanzu-yanzu: An ga wata a Najeriya, gobe za'a tashi da azumi: Kwamitin duban wata
Asali: UGC

KU KARANTA: Badaƙalar Kuɗin Makamai: Daga ƙarshe, shugaban Sojoji COAS ya bayyana a gaban yan majalisa

Asali: Legit.ng

Online view pixel