An bayyana Shugabannin Afirka mafi tsufa a 2021 tare da hotuna da ainahin shekarunsu

An bayyana Shugabannin Afirka mafi tsufa a 2021 tare da hotuna da ainahin shekarunsu

Wasu kasashe a Nahiyar Afirka sun nuna cewa karin maganar da ake yi na cewa shekaru ba komai bane face adadi ma tasiri a bangaren shugabanci. Da alama ba su damu da shekarun shugabannin da suka zaba don jagorantar su ba.

Jaridar Legit.ng ta kawo muku sunayen wadannan kasashen 7 a cikin Afirka tare da ainihin shekarun zababbun shugabannin su.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: FG ta bada muhimmiyar sanarwa game da rijistar NIN

An bayyana Shugabannin Afirka mafi tsufa a 2021 tare da hotuna da ainahin shekarunsu
An bayyana Shugabannin Afirka mafi tsufa a 2021 tare da hotuna da ainahin shekarunsu Hoto: Patrick Robert, Olivier Douliery-Pool, Waldo Swigers, Sean Gallup
Asali: Getty Images

1. Paul Biya (Kamaru)

An haifeshi a ranar 6 ga watan Nuwamba, 1982. A yanzu Paul Biya yana da shekaru 88 kuma har yanzu yana shugabantar kasar Kamaru.

Shugaban Kamaru na biyu shine na 7 a cikin jerin tsofaffin shugabanni a duniya, a cewar Business Insider.

An bayyana Shugabannin Afirka mafi tsufa a 2021 tare da hotuna da ainahin shekarunsu
An bayyana Shugabannin Afirka mafi tsufa a 2021 tare da hotuna da ainahin shekarunsu Hoto: Patrick Robert
Asali: Getty Images

2. Alpha Condé (Guinea)

A yanzu haka yana da shekaru 83 (an haife shi a ranar 4 ga watan Maris, 1938), a cewar Wikipedia, Alpha Condé yana kan mukamin ne tun a ranar 21 ga Disamba, 2010 bayan ya shafe shekaru yana adawa a Guinea kuma bayan bai yi nasarar zama mataimakin shugaban kasa ba a 1993 da 1998.

An bayyana Shugabannin Afirka mafi tsufa a 2021 tare da hotuna da ainahin shekarunsu
An bayyana Shugabannin Afirka mafi tsufa a 2021 tare da hotuna da ainahin shekarunsu Hoto: Sean Gallup
Asali: Getty Images

3. Alassane Ouattara (Ivory Coast)

Mai shekaru 79 (1 ga watanJanairu, 1942) Ouattara shine na uku a wannan jerin. Shugaban mai digiri na uku kuma mai riƙe da digirgir a harkar tattalin arziki ya kasance a kan kujerar shugabancin Cote d'Ivoire tun daga shekarar 2011.

An bayyana Shugabannin Afirka mafi tsufa a 2021 tare da hotuna da ainahin shekarunsu
An bayyana Shugabannin Afirka mafi tsufa a 2021 tare da hotuna da ainahin shekarunsu Hto: Sean Gallup
Asali: Getty Images

4. Evaristo Carvalho (São Tomé and Príncipe)

Evaristo Carvalho, mai shekaru 78, ya hau karagar mulki a ranar 3 ga Satumbar, 2016 bayan ya gaji Manuel Pinto da Costa, shugaban São Tomé da Príncipe sau biyu.

Carvalho ya tsaya takarar shugaban kasar São Toméan a shekara ta 2011, yayin da yake kakakin majalisar dokoki amma ya zo na biyu da kashi 21.8 na kuri'un.

KU KARANTA KUMA: Budurwa da aka haifa da kafa daya da rabi ta koka, ta ce tana bukatar sabon kafa

An bayyana Shugabannin Afirka mafi tsufa a 2021 tare da hotuna da ainahin shekarunsu
An bayyana Shugabannin Afirka mafi tsufa a 2021 tare da hotuna da ainahin shekarunsu Hoto: Horacio Villalobos - Corbis/Corbis
Asali: Getty Images

5. Muhammadu Buhari (Najeriya)

Muhammadu Buhari, mai shekaru 78 (an haife shi a ranar 17 ga watan Disamba,1942), an zabe shi ne ta hanyar dimokiradiyya a shekarar 2015 bayan takara uku ba tare da nasara ba a 2003, 2007, da kuma babban zaben 2011.

Buhari ya yi aiki a matsayin shugaban kasa daga ranar 31 ga Disamba, 1983, zuwa 27 ga Agusta, 1985 bayan ya karbi mulki a wani juyin mulkin soja.

An bayyana Shugabannin Afirka mafi tsufa a 2021 tare da hotuna da ainahin shekarunsu
An bayyana Shugabannin Afirka mafi tsufa a 2021 tare da hotuna da ainahin shekarunsu Hoto: Olivier Douliery-Pool
Asali: Getty Images

6. Nana Akufo-Addo (Ghana)

An haife shi a ranar 29 ga Maris, 1944, Akufo-Addo ya fara tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2008 sannan ya sake yin takara a shekarar 2012.

Ya yi nasara a yunkuri na uku ne ta hanyar kayar da wani matashin yaro John Dramani Mahama a zaben shekarar 2016.

An bayyana Shugabannin Afirka mafi tsufa a 2021 tare da hotuna da ainahin shekarunsu
An bayyana Shugabannin Afirka mafi tsufa a 2021 tare da hotuna da ainahin shekarunsu Hoto: Paul Marotta
Asali: Getty Images

7. Yoweri Museveni (Uganda)

Yoweri Museveni na Uganda ya cike jerin sunayenmu na 7. Dan shekaru 76 din (15 ga Agusta, 1944) yana daya daga cikin shugabannin da suka fi dadewa a karagar mulki. Ya kasance kan kujerar mulki tun 1986.

An bayyana Shugabannin Afirka mafi tsufa a 2021 tare da hotuna da ainahin shekarunsu
An bayyana Shugabannin Afirka mafi tsufa a 2021 tare da hotuna da ainahin shekarunsu Hoto: Waldo Swiegers
Asali: Getty Images

A gefe guda, Jam’iyyar APC reshen kasar Ingila, ta karyata wani labarin karya na kafofin sada zumunta cewa wasu ‘yan Najeriya sun mamaye gidan da shugaba Buhari yake a Landan don nuna adawa da Shugaban.

Jaridar Punch a jiya ta ruwaito cewa shugaban ya tashi daga Najeriya zuwa Landan inda zai kwashe makonni biyu domin duba lafiyarsa.

Wani a dandalin Twitter, @Tqswaggerboi, ya watsa hotunan wasu masu zanga-zanga tare da ikirarin cewa suna jiran isowar Buhari Fadar Najeriya ne a Landan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel